Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Jiha

Ziyarar neman hadin kai da goyon baya: Kungiyar Kwararrun Musulmai ta zo nan BRC

Lukman Adam

Kungiyar musulmi Kwararru, ta bidi goyon bayan gidan rediyon Bauchi – BRC, don kara inganta ayyukanta a duk fadin Jihar Bauchi.

Sakataren Kungiyar Malam Sulaiman Imrana ne yayi wannan roko, lokacin da Tawagar Kungiyar ta kai ziyarar ban girma wa Mahukuntan gidan rediyon.

Mal. Imrana ya lissafa harkokin Kungiyar da suka hada da shirya laccar kafin shigan watan Ramadan, shirya darussa da bada horo ga dalibai, ziyartar gidajen marayu, asibitoci da makabartu, akwai kuma zuwa da’awah a yankunan karkara masu wuyan shiga.

Sakataren Kungiyar ya kuma jinjina yadda BRC ke yada hidimomin dake da nasaba da addini a duk fadin jihar Bauchi, don haka ya nemi goyon bayan gidan rediyon, don kara yada hidimomin Kungiyar.

Da yake maida jawabi, Manajan Daraktan BRC Alh. Cindo Waziri, ya bayyana gamsuwa da yadda Kungiyar ke gudanar da harkokinta, don taimaka wa musulmi sauke nauyin da addininsu ya dora musu.

Ya kuma jinjina anfani da sabbin fasahohin zamani da Kungiyar keyi, don kyautata harkokinta, yana mai kiran su dore akan haka.

Alh. Waziri yayi alkawarin baiwa Kungiyar dukkan goyon bayan da take bida, don gudanar da harkokinta yadda ya kamata a duk fadin jihar Bauchi. Ya kuma yaba wa wakilan Kungiyar bisa ziyarar tasu, yana mai addu’ar Allah Ya saka musu da alkhairi.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com