Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Jiha

Zabubbukan cike gurbi na shekarar 2024: Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta tattauna da masu ruwa da tsaki

Rabiu Ishaq Mohammed

A shirye shiryenta na gudanar da zaben cike gurbi a wasu Jihohin kasar nan da lamarin ya shafa, Hukumar zabe ta kasa INEC ta gana da Kwamitin tuntuba tsakanin Hukumomi game da batun tsaro da matakan tabbatar da zaman lafiya a lokacin zabe a Jihar Bauchi, wanda aka shirya gudanarwa ran uku ga watan gobe na Fabrairun 2024.

Wannan batu na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hanun Shugaban sashen ilmantarwa da yada labarai an Hukumar ta INEC Mal. Aliyu Hassan Shaba, wadda kuma aka raba wa manema labarai, a shirye shiryen gudanar da zabukan cike gurbin mazabu hudu a Majalisar Dokokin Jihar, wadanda suka hada da Bauchi, Zungur/Galambi, Madara/Chinade da Ningi.

Kwamishinan zabe na Hukumar INEC Mr. Muhammad B. Nura da takwaransa na Rundunar ‘yansanda a Jiha Mr. Auwal Muhammad da dukkan mambobi, sunyi alkawarin yin aiki tare, don tabbatar tsaron ma’aikatan wucin-gadi da kayan zabe, da ma masu kada kuri’a, kafin, yayin da bayan zaben. Mambobin Kwamitin, cikin wata sanarwa sunyi kira ga masu kada kuri’a da su fito kwai-da-kwarkwata su sauke nauyin dake kansu na ‘yan kasa, wajen zaben wakilansu a Majalisar Dokokin jiha, wadanda suke son su wakilci mazabunsu hudu da za’a gudanar da zaben.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com