Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Tsaro

Yan Sanda Sun Bankado Wani Shirin Kona Gidan Gwamnatin Jihar Kano

 

Rundunar ‘yan sanda, ta ce ta gano wani shiri na kona gidan gwamnatin Kano da wasu bata gari ke kitsawa a kan shari’ar da ake ci gaba da yi a kotun koli kan zaben gwamna tsakanin jam’iyyar NNPP da APC.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a wani taro da shugabannin kafafen yada labarai, gabanin zaman kotun koli na daukaka kara kan shari’ar kujerar gwamnan Kano da aka gudanar a ranar Alhamis 21 ga watan Disamba 2023 a Abuja.

Gumel ya bukaci kwararrun kafafen yada labarai da su sanar da jama’a yadda ya kamata a kan abubuwan da ke faruwa bisa tsari da gaskiyar labari har zuwa ranar karshe na Yanke hukunci.

A cewarsa bai kamata a samu tashin hankali a Kano ba domin maganar tana kotun koli da ke Abuja ba a jihar ba.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com