Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran KasaTsaro

yan gudun Hijira fiye da dubu tara ne Gwamnatin jihar Bauchi da karba,

yan gudun Hijira fiye da dubu tara ne Gwamnatin jihar Bauchi da karba, wadanda suka tsero daga Mangu, Bokos da Barikin Ladi a Jihar Plato, sakamakon tashin hankali dake can.

Kwamishinar harkokin jin kai da magance musibu Hajiya Hajara Yakubu Wanka ce ta bayyana hakan a Karamar hukumar Toro, lokacin da ta jagoranci jami’an Ma’aikatar, zuwa ziyarar jaje da rabon kayan abinci da sauran kayan bukaru, ga wadanda lamarin ya shafa a yankin.

Hajiya Hajara Wanka, wacce ta bayyana damuwar gwamnatin jihar game da karuwar rikice rikice a makwabciyar jihar, tayi kiran samun hakuri da juna tsakanin mabiya addinai, siyasa da kabilu daban daban a yankin, don samun ingantuwan zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan jihar.

Kwamishinar tayi kira ga ‘yan gudun Hijiran su kwantar da hankali, tana mai basu tabbacin shirin gwamnatin jiha, karkashin jagorancin Sanata Bala Mohammed na yin iya bakin kokarinta, don tallafa musu, kafin su koma yankunansu daban daban.

Ta sanar da gudummawar gwamnatin jiha ta naira sama da miliyan guda, buhunan masara da shinkafa, sama da dari daya, barguna, tabarmi, man girki, bokatai gishiri, magi da farantai da sauransu, wadanda za’a raba wa ‘yan gudun Hijiran dake sansanoni biyar a Karamar hukumar ta Toro, tana mai gargadin tabbatar da ganin anyi rabon tsakani da Allah.

Da yake marabtar Tawagar Kwamishinar, Shugaban Kwamitin rikon Majalisar Karamar Hukumar Alhaji Dallami Garba Abubakar, wanda Mataimakinsa Hon Idris Abdullahi Tama ya wakilta, ya yaba wa gwamnatin jiha bisa wannan karimci, kuma yayi alkawarin rabon kayayyakin da aka samar bisa adalci.

Alh. Danlami Abubakar yace Karamar Hukumar Toro ta tsugunar da dubban ‘yan gudun hijira a wasu yankuna da suka hada da Toro,, Tilde, Goljaredi, Kara, Panshanu, Takanda da sauransu.

 

 

 

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com