Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Ilimi

Wani malamin addini Musulunci ya shawari iyaye suna tura yaran su Makaranta domin tashi da Tarbiya

Wani malamin addinin Musulunci imam Adamu Y liman ya tunatas da al’ummar musulmi, ta tura ‘ya’yanta zuwa makaranta, domin su taso da tarbiyya ta gari a tsakanin mutane.
Imam Adamu yayi wannan tunatarwa ce, yayin wata walima da wasu daliban da suka sauke karatu a Gidauniyar ilimi ta AbdulMumini dake Alkaleri suka shirya.

A cewarsa, gado mafi alkhairin da za’a bari wa ‘ya’ya, ba tarin kudi ko dukiya, ko manyan gidaje bane, ilimi ne, wanda zai taimaka musu anan duniya da gobe kiyama.

Don haka ne yayi kira ga iyaye su tura’ ya’yansu zuwa makarantun islamiyya da na boko, don su sami kyakkyawar rayuwa abar koyi.

Sannan kuma imam Adamu Y liman, ya bukaci daliban da suka kammala karatun, su kasance masu tsoron Allah a rayuwarsu ta yau da kullum, kuma su kasance masu kwatanta koyarwar al-Qurani mai girma da Hadisan Manzon Allah Muhammadu S. A. W. Sannan kuma su kwan da sanin cewa yanzu ne suka fara neman ilimin yadda zasu bauta wa Allah, kuma sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi.

Related Articles

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com