Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
LabaraiLabaran Jiha

Uwar gidan Gomnan Jiha ta marabci majalisar kungiyar mata ta kasa.

Amina Umar

Uwar gidan Gwamnan jiha Hajia A’isha Bala Muhammad tayi alkawarin bada fifiko ga batutuwan da suka shafi mata a wannan jiha. Ta bayyana haka ne lokacin da ta marabci Majalisar Kungiyar mata ta kasa – NCWS Reshen jiha a Gidan Gwamnati dake Bauchi.

Uwar gidan Gwamnan jihar, tace wajibi ne Kungiyar ta NCWS ta kara jan damarar tallafa wa mata, don su zama masu dogaro da kansu, bisa la’akari da kalu-balen da ake fiskanta, inda mata ne suka zama masu fiskantar barazana. Tana mai karawa da cewa koda yaushe kofarta zata kasance a bude fallau, don karban shawarwari masu ma’ana da zasu taimaka wajen ginawa da bunkasa Kungiyar NCWS a wannan jiha.

Tun farko, Shugabar Kungiyar NCWS Reshen Jihar Bauchi, Hajia Jummai Liman Bello ta yaba wa Uwar gidan Gwamnan, bisa tallafin da take baiwa mata da kananan yara a wannan jihar. Sannan tace maksudin ziyarar shi ne, taya Uwar gidan Gwamnan bisa nasarar da Gwamna Bala Muhammad ya samu ne a Kotun koli.

Ta kuma tabbatar da cewa Kungiyar ta NCWS zata cigaba da mara baya wa Uwar gidan Gwamnan a kokarinta na taimako da karfafa gwiwar mata da matasa a Jihar Bauchi.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com