Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Duniya

USAID ZATA BADA HORO DON INGANTA ILIMI A BAUHCI.

Daga Musilm Lawan

 

Hukumar raya kasashe ta kasar Amurka – USAID ta ayyana shirinta na taimaka wa Jihar Bauchi ta hanyar bada horo, don ta cimma manufarta na kawo sauye sauye a harkar ilimi.

Wata Babbar Jami’ar Hukumar Mariam Britel ce ta sanar da haka, lokacin da jagoranci sauran mambobin Ofishinta zuwa ziyarar wayar da kai ga Gwamnan Jiha Sanata Bala Muhammad a Gidan Gwamnatin Jiha dake Bauchi.

Tace Hukumar USAID ta kwashe fiye da shekaru goma tana aiki a Jihar Bauchi, inda tafi maida hankali a muhimman bangarori, don haka akwai bukatar tallafa wa sauye sauyen da gwamnatin jihar keyi a bangaren ilimi, da nufin cimma manufa.

Da yake maida martani Gwamna Bala Muhammad ya shaida irin gudumawar da USAID ke baiwa Jihar Bauchi a bangarorin bada horo wa ma’aikata, kayan koyarwa a makarantu da sauran muhimman bangarori, yana mai alkawarin yin anfani da wannan dama yadda ya kamata don cimma muradun wannan jiha da al’ummarta.

Zuwa yanzu, Gwamnan yace bisa la’akari da tabbacin da aka samu daga Hukumar USAID, nan ba da jimawa ba, Gwamnatin jiha zata aiwatar da shawarwarin da Taron koli kan makomar ilimi a wannan jiha ya gabatar, wanda aka gwamnatinsa ta gudanar.

A Wani labarin Kuma

Gwamna Bala Muhammad ya bada tabbacin cikakken goyon bayan gwamnatinsa, wajen samun nasarar aiwatar da Shirin inganta kiwon dabbobi a wannan jiha.

Gwamnan ya bada wannan tabbaci ne, lokacin da ya marabci masu ruwa da tsaki daga Bankin duniya da Ma’aiaktar noma da wadata kasa da abinci ta Tarayya, karkashin jagornacin Jami’in Shirin na kasa Mal. Sanusi Abubakar a Majalisar zartaswa ta Gidan Gwamnati dake Bauchi.

Gwamna Bala ya bayyana gamsuwar cewa Jihar Bauchi ta dade tana cin moriyar ayyukan Bankin duniya, kuma yayi maraba da shigar da Jihar Bauchi a matsayin wadda zata ci gajiyar Shirin. Yace aiwatar da shirin a Bauchi, zai taimaka wa gwamnatinsa ta cimma muradunta a bangaren kiwon dabbobi, kuma yayi alkawarin samar da dukkan abubuwan da ake bukata don aiwatar da shirin.

Gwamnan ya baiwa Tawagar Shirin a Bauchi, umurnin yin aiki tare da Shirin inganta noma a kasashe masu zafi na ACRESAL a wannan jiha, don cimma bunkasa noma, ta yadda za’a takaita kalu-balen da ake fiskanta a sashen.

Tun farko, Jami’in Shirin na kasa Mal. Sanusi Abubakar yace Tawagar ta zo Bauchi ne, don duba matsayin yadda Shirin ke gudana, kuma ya yaba wa Gwamna Bala Muhammad, bisa yadda ya samar da fili mai fadin kadada 200 wa Shirin, don aiwatar da harkokinsa.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com