Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
IlimiLabaran Kasa

Uban Jami’ar ATBU yayi kira ga Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da manufofin da zasu kawo sauyi a Jami’o’in Nigeria.

Uban Jami’ar ATBU ta Buuchi Adeyemo Adejudge yayi kira ga Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da manufofi da shirye shiryen da zasu kawo sauyi a Jami’o’in Nigeria, don magance kalu-balen zamani da ake fiskanta, da nufin samun cigaba cikin sauri a kasar nan.
Adejudbe yayi wannan kiran ne, yayin bikin yaye daliban Jami’ar ATBU ta Bauchi karo na 26, 27, 28 da 29 a hade, wanda akayi a Dandalin yaye dalibai na Jami’ar dake Gubi a Buuchi.

Uban Jami’ar, kuma Ewi na Ado-Ekiti, ya kuma tabbatar da shirin Jami’ar na cigaba da samar da ilimi mai nagarta da tarbiyya ta kwarai ga dalibanta, da nufin mara baya wa gwamnatoci, masu kokarin raya al’umma.
Ya jinjina wa Gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu, da ta fara biyan rarar albashin ma’aikatan Jami’ar, yana mai kiran samar da karin taimako a Cibiyoyin, don su samu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, bisa la’akari da yadda sha’anin tattalin arziki ke cigaba da sunkayawa a kasar nan.

Uban Jami’ar, wanda ya samu wakilcin Shugaban Jami’ar ta ATBU Prof. Muhammad Ahmad AbdulAziz, yayi anfani da wannan dama, ya baiwa iyaye shawarin rungumar hakkinsu na iyaye, wajen tabbatar da ganin ‘ya’yansu sun samu shiga makarantu, kuma su sanya ido akan kai-komonsu, musamman a leke-leken da sukeyi a shafukan sada zumunata, domin su zama shugabanni na kwarai a gobe.
Uban Jami’ar ya kuma bayyana gamsuwarsa ga Gwamna Bala Muhammad na jiha, da Gwamnan jihar Katsina Dr. Umar Dikko Raddah, Sarakuna da sauran manyan bakin da suka halarci

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com