Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
LabaraiLabaran JihaLafiya

Tsaftar Muhalli a Jihar Bauchi: Hukumar da abin ya shafa ta Jaddada kudirin Gomnatin jiha

Isah Muhammad Jungudo

Gwamnatin Jiha zata fidda sabuwar manufar kula da muhalli, wadda zata fayyace matakan gudanar da aikin tsabtar muhalli ta wata-wata a duk fadin wannan jiha.
Kwamishinan Ma’aikatar gidaje da muhalli na jiha Hon. Danlami Ahmad Kawule ne ya sanar da haka, lokacin da yake duba yadda aikin tsabtar muhallin wannan wata ke gudana, a cikin garin Bauchi. Yace sabuwar manufar, in aka aiwatar da ita, zata magance inda ake fiskantar matsaloli, ta kuma tabbatar da cikakkiyar biyayya daga jama’a. A cewarsa, dukkan masu ruwa da tsaki zasu samu rawar takawa a cikin sabuwar manufar.
Shi ma cikin tsokacinsa, sabon Babban Daraktan Hukumar kare muhalli ta jiha – BASEPA Dr. Mahmud Muhammad Bose, ya bayyana gamsuwarsa game da yadda mutane suka fito don gudanar da aikin tsabtar muhallin na wata-wata. Yana mai cewa lokacin da aka fara aiki da sabuwar manufar, Shugabannin al’umma da Ma’aikatu zasu taka rawa sosai a sha’anin gudanar da aikin tsabtar muhallin na wata-wata a duk fadin wannan jiha.
Babban Daraktan na BASEPA, yayi kira ga mutane su cigaba da gudanar da aikin tsabtar muhallin na wata-wata, kamar yadda aka umurcesu.
Shi ma Shugaban Kungiyar makanikan mota ta Nigeria Reshen Kasuwar Muda-Lawal ta Bauchi Alh. Salisu Alin-Bababa, cikin jawabinsa, ya yaba wa Hukumar ta BASEPA, bisa taimakonsu da tayi da kayan aikin tsabtar muhalli.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com