Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Jiha

TARON BITA DON KARA KWAZON ‘YAN JARIDAN GIDAN GWAMNATI.

A wani yunkurin tabbatar da kwatanta kwarewa a yayin yayata manufofi da shirye shiryen Gwamnatin Jihar Bauchi, mambobi Tawagar ‘yanjarida na Gidan Gwamnatin jiha sun samu horo a wani taron bita na ini uku, game da sabbin dabarun aikin jarida da suke bullowa.

Taron bitar wanda akayi wa taken ‘Mambobin Tawagar ‘yan jaridan gidan gwamnati da kalu-balen yada manufofi da shirye shiryen gwamnati yadda ya kamata a karni na 21, gwamnatin jiha taga ya dace ta kara inganta kwazon Tawagar ‘yan jaridan.

Da yake bude taron a Jos Fadar Jihar Plato, Gwamna Bala Muhammad yace samar da alaka ta kwarai tsakanin Gwamnati da ‘yan jarida a wanann jiha, har gobe shi ne muradin gwamnatinsa.

Gwamna Bala Muhammad wanda ya samu wakilcin Kwamishinan yada labarai da sadarwa Comrade Usman Danturaki, ya bayyana kwarin niyyarsa, ba kadai ga jin dadin ma’aikata ‘yan jarida ba, har ma karfafa musu gwiwar kara inganta aikinsu.

A nasa tsokacin, Mai baiwa gwamna shawari na musamman ta fiskar yada labarai Comrade Mukhtar Gidadeo, wanda yayi kira ga mahalartan da suyi anfani da wannan damar yadda ya kamata, ya kuma yaba wa Gwamna Bala Muhammad, bisa yadda ya kara inganta taron bitar.

Cikin jawabansu na fatan alkhairi, Daraktan yada labarai da kula da harkokin jama’a na Gwamnatin Jihar Plato Mr. Gyang Bere da Wakilin Shugaban Kungiyar ‘yan jarida ta Nigeria NUJ na Jihar Mr. Pam Musa, ya bayyana taron bitar a matsayin wata kira ga saura don suyi koyi.

Da yake jawabi a madadin mahalartan, Shugaban Tawagar ‘yan jaridan Mr.John Habila Mure na Gidan Talabijin na Jiha – BATV ya bada tabbacin yin anfani da ilimin da suka samu ta hanyar da ta kamata wajen kara inganta rahotannin da suke bayarwa.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com