Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
IlimiLabaran Kasa

Shugaba Bola Ahmad Tinubu yayi alkawarin shirin gwamnatinsa, don inganta matsayin ilimi a kasar nan.

Shugaba Bola Ahmad Tinubu yayi alkawarin shirin gwamnatinsa zatayi anfani da dan abin dake hanunta, don inganta matsayin ilimi a kasar nan, kamar yadda lamarin yake a duniya.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne, yayin bikin yaye daliban Jami’ar ATBU ta Bauchi, karo na 26 da 27 da 28 da 29, wanda ya gudana a Dandalin yaye dalibai dake matsugunin Jami’ar na Gubi a Bauchi.
Shugaban, wanda ya samu wakilcin wani Darakta a Ma’aikatar ilimi ta T arayya Mr. James Achedo yace Jami’o’in Nigeria sunyi fama da mawuyacin hali a shekarun da suka gabata, sakamakon yawan daukan matakin yaje-yajen aiki, don haka akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta maida hankalinta kan samar da yanayi mai kyau, don wanzar da tattaunawa da Kungiyoyi, da nufin kawo karshen takaddamar.
Shugaba Tinubu, yayi kira ga Jami’ar ta ATBU ta hanzarta hada kai da Jami’o’i a duk fadin duniya, don musayar ra’ayoyi da ayyukan binciken da zasu anfanar da kasar nan. Yana mai jinjina nasarorin da Jami’o’in Nigeria suka samu, kuma ya tabbatar da shirin gwamnatin Tarayya na cigaba da samar da kudade masu tsoka wa sashen ilimi, musamman ta fiskar bincike, ta yadda daliban da suka kammala karatu zasu cigaba da gogayya da juna, a wannan duniya mai sauyawa a kowane lokaci.
Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya bukaci Jami’ar ATBU, a matsayinta na Jami’ar fasahar zamani, ta bullo da dabaru na kwarai, wadanda zasu samar da mafita irin ta fasahar zamani ga dimbin kalu-balen da kasar nan ke fiskanta.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com