Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labarai

SHIRIN SAMAR DA AIKI NA KASA – NDE RESHEN JIHA YA FARA HORAS DA MARASA AIKI

SHIRIN SAMAR DA AIKI NA KASA – NDE RESHEN JIHA YA FARA HORAS DA MUTANE MARASA AIKI YADDA AKE KIWON DABBOBI DA SARRAFA IRIN SHUKA.

Sashen samar da aiki na Kasa – NDE Reshen jiha, ya fara horas da mutane marasa aiki su dari daya, kan yadda ake kiwon dabbobi da samar da irin shuka, karkashin Shirinsa na koyar da dabarun noma masu dorewa.

Da yake magana a wajen bada horon da kuma kaddamar da Shirin na bana a Bauchi, Babban Darakta Hukumar ta NDE Alh. Abubakar Nuhu Fikpo, yace horaswar zata baiwa matasa damar samun ilimin yadda zasu kafa harkokin kasuwancinsu masu nasaba da noma.

Alh. Fikpo, wanda ya samu wakilcin Jami’in Shirin a wannan jiha Malam Lawal Ali Yaya a wajen taron, yace mutane dari daya ne, zasu kwashe watanni uku suna samun cikakken horo, kan kiwon dabbobi da sarrafa irin shuka da suka zaba.

Cikin jawabinsa, Daraktan Sashen dabbaka samar da aiki a yankunan karkara na Hukumar ta NDE Mr. Edem O. Duke, wanda shi ma Mr. Nkem Ekeamadi ya wakilta a wajen taron, ya bayyana cewa, an tsara Shirin ne, don cusa sabbin dabaru da kirkire kirkiren noman zamani, tare da dukkan alfanun dake tattare dasu, domin mutane marasa aikin su dogara da kansu.

Cikin jawabinsa na fatan alkhairi, Mai martaba Sarkin Bauchi Alh. Rilwanu Sulaiman Adamu, ta bakin wakilinsa kuma Sarkin Office na Bauchi Zubairu Aliyu, ya yaba wa yunkurin na Hukumar NDE, na zaben Bauchi, a matsayin daya daga cikin Jihohin da zata ci moriyar Shirin a Tarayyar kasar nan.

Sarkin, yayi kira ga mahalartan, su maida hankali sosai, kuma su dauka wannan wata dama ce suka samu ta musamman, don haka su kara maida hankali sosai akan horon.

Wasu daga cikin mahalartan da aka zanta dasu, sun bayyana cikakken farin cikinsu ga Hukumar NDE da Gwamnatin Tarayya, bisa karimcin da suka musu, kuma sunyi alkawarin yin anfani da bashin da za’a basu yadda ya kamata, bisa sharadin da aka shimfida.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com