Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Jiha

Sata da cinikayyar Yara kanana a jihar Bauchi: Majalisar dokoki ta Magantu.

Rabi'u Ishaq Mohammed

Majalisar Dokokin jiha ta bayyana damuwa game da gungun wasu miyagu da suka kware a sata, safara da cinikin yara kanana daga Jihar Bauchi zuwa wasu sassan kasar nan. Wannan batu ya zo ne, a karkashin batutuwan da ke da muhimmanci da suka shafi rayuwar al’umma, wanda Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Kirfi Hon. Habib Umar ya gabatar a yayin zaman Majalisar.

Yace miyagun sun dade suna gudanar da mugun aikinsu, sama da shekaru goma, kuma ana zargin sun goge akan sata, ciniki da safarar mutane, musamman kananan yara tsakanin jihohi. A cewarsa, yara bakwai da aka sace daga jihar Bauchii kuma akayi safararsu zuwa jihar Kano, tuni aka sake maidasu zuwa iyayensu na asali.

Hon. Habib Umar ya yaba wa kokarin Rundunar ‘yansanda a Jihar Kano, kuma yayi kira ga iyaye su cigaba da sanya ido kan ‘ya’yansu a matsayin babban hakkin dake kansu kenan. Sannan ya bukaci gwamnatin jihar Bauchi, ta dauki matakin shari’a mai tsauri akan wadanda ake zargi da hanu da aka kama, kuma ta umurci rufe Asibitin nan mai zaman kansa, wanda ake zargin yana da hanu cikin safarar jarirai a nan Fadar jiha.

Cikin hukuncin da ya yanke, Kakakin Majalisar Hon. Babayo Muhammad Akuyam, ya mika batun ga Kwamitin hadin gwiwa na lafiya, tsaro da harkokin mata na Majalisar, don gudanar da bincike mai zurfi, kuma ya baiwa gwamnatin jiha shawarar daukan matakin shari’a da ya dace, don tabbaar da ganin wadanda ake zargin sun gurfana a gaban alkali.

A halin da ake ciki, Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Ganjuwa ta gabas a Majalisar dokokin jiha Hon Dayyabu Ladan Muhammad ya roki gwamnatin jiha ta daga darajar Cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta Soro zuwa matakin Babban Asibiti. Yayi wannan roko ne cikin wata bukata da ya gabatar a yayin zaman Majalisar karkashin jagorancin Kakakinta Hon. Babayo Muhammad.

A cewarsa, akwai bukatar daga darajar Cibiyar, bisa la’akari da bukatar hakan, don hakan zai samar da yanayin da ake bukata don gudanar da aiki cikin sauki, ga ma’aikatan lafiya da majinyatan baki daya. Yace in aka daga darajar Cibiyar zuwa Babban Asibiti, za’a samu sashen kulawa na gaggawa da sauran ayyukan kula da lafiya na musamman.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com