Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran KasaTattalin Arziki

Rahoton Tattalin Arzikin Afirka Na 2023 Ya Nuna Bukatar Gyaran Fuska A Nahiyar Don Samun Ci Gaba Mai Dorewa

Daga  Alhaji Abubakar from Bauchi

Rahoton Tattalin Arziki na Afirka 2023 (ERA 2023) ya bayyana cewa, akwai bukatar yin kwarya-kwaryan gyaran fuska domin samun ci gaba mai dorewa da kuma jajircewa don cimma nasarar da ake fatan gani.

Har ila yau, rahoton ya ce: “Manufofin masana’antun da suka bunkasa na buƙatar mayar da hankali ga sassan biyu da kuma samun daidaitattun abubuwa na yau da kullum. Sannan yana da mahimmanci ƙasashen yankin su gano ingantattun hanyoyin haɗin kai da dabarun aiwatar da manufofin ci gaba don haɓaka harkokin masana’antu.”

Rahoton mai taken: “Gina gurbin Afirka da ya dace wajen bunkasa tattalin arzikin duniya”, wanda Darakta mai kula da harkokin tattalin arziki da mulki a hukumar kula da tattalin arzikin Afirka ta Majalisar Dinkin Duniya (UNECA), Adam Elhiraika, ya gabatar a Abuja ranar Litinin, ya nuna cewa, tsarin ci gaban tattalin arzikin duniya a halin yanzu yana ba da mamaki ga kasashen Afirka bisa yadda suke da bukatar hanzarta habaka masana’antu ta hanyar yin gwaji da kyau kan abin da zai fi zama mafita gare su da kuma yadda za su daidaita lamarin bisa tsarinsu na gida.

Elhiraika ya bayyana cewa, ci gaban da ake samu a Afirka yana da alaƙa da fitar da kayayyaki, yin aiki da manya kasashen duniya da kamfanoni, da bin ka’idoji da kuma haɓaka ƙungiyoyin masana’antu.

Waɗannan abubuwa, bisa ga rahoton na ERA 2023, ana bukatarsu a bangarori daban-daban ta fuskar ire-iren kamfanonin da ake da su da kuma ƙarfin fasaharsu.

A nashi bangaren, Babban Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mista Matthias Schmale, wanda Masanin Tattalin Arziki, Nonso Obikili, ya wakilta, ya lura cewa abubuwa marasa dadi daban-daban, kamar illolin da annobar COVID-19 ta haifar, da yunkurin mamayar da Rasha ke yi a Ukraine, da sauyin yanayi ya sa Afirka ta fuskanci koma-baya wajen cimma muradun ci gaba mai dorewa na duniya (SDGs).

Ya ba da misali da yadda talauci a cikin 2021 ya karu sosai, lokacin da kusan ‘yan Afirka miliyan 30 suka fada kangin matsanancin talauci, inda hakan ya haifar da asarar ayyuka miliyan 22.

“Kasashe goma da suke da mafi yawan matalauta sun kai kashi 64.7% na nahiyar. Kasashe hudu na farko—Nijeriya (miliyan 100), Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo (miliyan 67), Tanzaniya (miliyan 36), da Habasha (miliyan 33)—sun dauki kashi 42% na talakawa da kef ama da talauci.” In ji Schmale.

Don haka, ERA 2023 ya yi kira da a samar da sabbin dabaru ga kasashen Afirka don magance kalubalen matsalar tattalin arzikin duniya. Rahoton ya yi kira da a inganta yadda ake magance matsaloli da samar da jajircewa ta hanyar tsare-tsare masu kyau na ci gaban kasa da shugabanci nagari, da kuma kawo sauyi ga tsarin ci gaban masana’antu.

Bugu da kari, Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki, Dokta Tope Fasua, ya bayyana koma-bayan tattalin arzikin da Nijeriya ta samu tun a shekarun baya da suka hada da: hauhuwar farashin kayayyaki a farkon shekarun 1970 bayan tashin gwauron zabon farashin mai a shekarar 1973; koma bayan shekarun 1980 saboda faduwar farashin kayayyaki; da kuma wani matsalar da aka samu a tsakiyar shekarun 2000 sakamakon faduwar danyen mai.

“Muna rayuwa cikin rashin daidaito ta fuskar tattalin arzikinmu, kuma yawancin Afirka har yanzu suna fama da irin wannan matsalar.” In ji shi.

Daga cikin wadanda suka halarci taron gabatar da rahoton akwai wakilan ofishin jakadancin Amurka, Tarayyar Turai, Sashen Bunkasa Ci Gaba na USAID, Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta Tarayya, Ma’aikatar Kudi, Babban Bankin Nijeriya da kuma hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com