Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Duniya

NDLE ta kama wata mata da albarusai zata Kai wa Yan bindiga

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa – NDLEA, tace ta katse hanzarin wata mace mai kimanin shekaru 28 da haihuwa Bilkisu Sulaiman, wacce take kai wa ‘yan bindiga albarussai.
Daraktan yada labarai na Hukumar Mr. Femi Babafemi, cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, yace sunan matar ce kan gaba, cikin jerin sauran wadanda ake zargi su 12 da Hukumar ta kama cikin wannan sabuwar shekarar, a ayyukan da ta gudanar a Jihohin Kaduna, Lagos, Niger, Kogi, Kano, Borno da Oshun.

Mr. Bababfemi, yace Jami’an Hukumar NDLEA sun kama matar ce a sintirin da sukeyi a kan babbar hanyar Zaria zuwa Kano, tana dauke da albarusai 249 kunshe a cikin wata bakar jakar leda, boye a cikin jakarta ta hanu.
Daraktan yada labaran, yace a Babban Filin saukar jiragen sama na Murtala Muhammad dake Lagos kuma, Jami’an Hukumar sun dakile wani kunshin ganyen wiwi ma karfin gaske, wanda aka boye cikin kayan dambe, wanda kuma akayi kokarin shigowa dashi daga Kasar Amurka.
A cewar sanarwar, kunshin, wanda aka masa alama da kayan dambe, ya iso kasar nan ne daga Birnin al-Qahira ran litinin daya ga wata, a cikin wani jirgin saman kasar Masar

 

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com