Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Jiha

Miyetti Allah: An bukaci mambobi da su kawo karshen takaddama a tsakanin su.

Shugaban Kwamitin rikon kwaryar Majalisar K/hukumar Alkaleri Comrade Bala Ibrahim Mahamoud, yayi kira ga Kungiyar Miyetti Allah Reshen Alkaleri da babban murya, ta hanzarta warware takaddamar shugabanci dake cikin Kungiyar.

Comrade Bala MAHAMOUD, yayi wannan kira ne, yayin wani taron da yayi da shugabanni da mambobin bangarorin dake husuma da junansu. A cewarsa, babu wani cigaban da za’a samu, ba tare da zaman lafiya da juna a kowace irin al’umma ba. Yana mai karawa da cewa ba zai taba lamuntar rashin adalci ba, kuma babu wani bangaren da za’a zalunta bisa kowane dalili. Don haka akwai bukatar Kungiyar ta hade kanta, tayi aiki karkashin inuwa daya, don samun cigaba mai ma’ana, don haka ya bukaci su sasanta ba tare da bata lokaci ba, kuma su bashi rahoto akan don ya zama shaida.

Shugaban ya kuma bukaci mambobin Kungiyar su tura ‘ya’yansu makaranta, domin su ma su zama mutanen kwarai. Yana mai kokawa da yadda aka bar al’ummar fulani a baya, ta fiskar ilimi. Don haka ya jaddada kira a garesu, su kai yaransu makarantar boko da ta Islamiyya, saboda su zama jakkadun kwarai ga Karamar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi da kasa baki daya.

Shugaban Kwamitin rikon yan kuma gargadi shugabannin Kungiyar ta Miyetti-Allah, kada su kyale baki su samu mafaka, ko gidaje su zama maboya, bisa kowane dalili, sannan su kai rahoton duk wani motsi, ko wani kunshin kaya da basu sakankance dasu ba, ga jami’an tsaro, don daukan matakin da ya dace cikin gaggawa.

Da yake kira a gare su da dukufa kan addu’a wa Gwamnan jiha senator Bala Abdulkadir Muhammad Kauran Bauchi CON, yayi nasara a kotun Koli, yace hakan na da muhimmanci, don cigaba da ayyukan alkhairi da yake yi wa al’ummar jihar Bauchi.

Shugabannin bangarorin, Alhaji Juli Kufa da Yahaya Kuncekura, sunyi alkawarin yin abin da ya kamata, don samun zaman lafiya, fahimtar juna da kwanciyar hankali a Karamar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi da Tarayyar Nijeriya baki daya.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com