Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Lafiya

Majalisar dokokin jihar Bauchi Zata magance matsalar Ayyukan sashin lafiya

Majalisar Dokokin jihar Bauchi tayi alkawarin magance matsalolin dake ci wa ayyukan sashen kula da lafiya a matakin farko na jihar tuwo a kwarya. Tana mai cewa hakan zai sa a samar da cikakkun dokokin da suka dace da tanade-tanaden dokar kula da lafiya ta kasa.

Shugaban Kwamitin kula da lafiya da jama’a na Majalisar Hon. Lawal Dauda ne ya sanar da haka, lokacin da ya jagoranci mambobin Kwamitin zuwa ran-gadin wasu Cibiyoyin kula da lafiya a jihar ta Bauchi. Yace Majalisar dokokin jihar ta goma, zata kulla kawance mai karfi da abokan jera tafiya ta fiskar raya kasa, kuma zata kafa dokoki masu karfi, don kara inganta ayyukan kula da lafiya.

Hon. Dauda, yayi ishara da cewa in aka samu fahimtar da ta dace, sashen kula da lafiya zai iya taka rawar gani, don daga martabar jihar Bauchi. Yana mai cewa Kwamitin ya lura da cewa, duk da muhimmancin da Cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko ke dashi, suna kuma fiskantar kalu-bale masu yawa, kama daga karancin kwararrun ma’aikata da karancin kayan aiki na kwarai, karancin hasken wutar lantarki da kuma karancin gidajen ma’aikata da sauran matsaloli.

A cewar Hon. Dauda, dokoki masu kwari suna taka rawa sosai a sawwarawa da karfafa tsarin kula da lafiya, ta hanyar dinke dokoki da manufofi yadda ya kamata. Yana mai lissafa sauran matakan da suka hada da samar da kudi akan kari wa sashen, tabbatar da samuwar kayan aikin da ake bukata, dafa wa ayyukan sa-ido na ‘yan Majalisa da nufin hanzarta jan hankalin masu sha’awar zuba jari a harkar ilimi, horaswa da magance karancin masu samar da ayyukan kula da lafiya a wuraren da basu dasu sosai da sauran bukatu.

Mambobin Kwamitin Sale Hodi mai wakiltar mazabar Disina, Ahmad Maikudi Yahya na mazabar Chiroma, Hamza Sa’idu na Mazabar Toro/Jema’a da Bello Sarki Jadori na mazabar Gamawa, suka ce tilas ne masu ruwa da tsaki su lura da muhimmancin rawar da bangaren shirya dokoki da bangaren Hukumomin kula da lafiya suke takawa, wajen kawo sauyi a fagen aikin kula da lafiya.

Cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko na karshe da Kwamitin ya ziyarta sune na Chinade a K/hukumar Katagum da ta Gumau a K/hukumar Toro.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com