Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran JihaLafiya

Majalisar Dokokin jiha ta jaddada shiri na ganin an kyautata bangaren kiwon lafiya a jihar Bauchi

Daga Rabiu Ishaq Mohammed

Kwamitin kula da lafiya da ma’aikata na Majalisar Dokoki ta jihar Bauchi ya bayyana shirinsa na tabbatar da ganin manufofin gwamnati sun karfafa cigaban ayyukan kula da lafiya a jihar Bauchi.

Shugaban Kwamitin Hon. Lawal Dauda ne ya bayyana haka, lokacin da ya kai ziyarar aiki tare da mambobin Kwamitin, a Cibiyoyin kula da lafiya na Tilden-fulani, Magama da Nabardo a Karamar Hukumar Toro, , Kofar-Ran a Karamar Hukumar Bauchi da Konkiyel a Karamar Hukumar Darazau

Yace Kwamitin na ziyarar aikin ne, don gane wa idonsa raunin da tsarin shugabancin Cibiyoyin suke dashi, don kuma ya bada shawarin yadda za’a shawo kan matsalolinsu a duk fadin jiha. Yana mai karawa da nuna damuwa game da mummunan yanayin da wasu Cibiyoyin suke ciki, sannan ya bada tabbacin baiwa gwamnati da Hukumomin da suka dace, shawarin yadda za’a magance matsalolin, ta yadda kwalliya zata biya kudin sabulu.

Shugaban Kwamitin ya bukaci Asibitocin su daga darajar kayan aikinsu zuwa tsarin zamani, yace hakan ita ce hanyar da ta fi dacewa da gudanar da aikin kula da lafiya ga al’umma.

Jami’an kula da lafiya a Cibiyoyin da Kwamitin ya ziyarta, sun shaida wa Kwamitin cewa suna fama da matsaloli masu yawa, da suka hada da karancin ma’aikata, rashin hasken wutar lantarki, rashin kayan aiki a dakunan gwaje-gwaje da sauran matsaloli makamanta. Kuma sunyi anfani da wannan dama sukayi kira ga gwamnatin jihar Bauchi, ta taimaka musu su shawo kan matsalolin, domin suji dadin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Tun farko, Kwamitin ya ziyarci Ofishin Shugabannin Kwamitocin rikon Majalisun Kananan Hukumomin da ya ziyarta na Toro, Bauchi da Darazo

Da suke marabtar Kwamitin a Ofisoshinsu daban daban, Shugabannin Kananan Hukumomin, sunyi alkawarin mara baya wa kokarin gwamnatin jiha na samar da nagartaccen aikin kula da lafiya ga kowa da kowa.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com