Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Jiha

KWAMISHINAN YADA LABARAI NA JIHAR BAUCHI YA TABBATAR DA SHIRIN GWAMNATIN JIHA NA SAMAR DA AIKIN YI GA MATASA

DAGA OKASHA DANMADAMI:

Kwamishinan yada labarai da sadarwa Comrade Usman Garba Danturaki, ya tabbatar da shirin gwamnatin jiha ta yau, na samar da ayyukan yi ga dimbin matasan wannan jiha. Ya bayyana haka ne lokacin da yake amsar lambar yabo daga Kungiyar raya kauyen Wandi dake cikin K/hukumar Dass.

Honourable Usman Garba Danturaki, Kwamishinan Yada labarai na Jihar Bauchi

Comrade Danturaki yace nasarorin da Gwamnatin Bala Muhammad ta cimma, bata samun cimma hakan ba, ba tare da goyon baya da hadin kan galibin al’ummar wannan jiha ba. Yana mai cewa Allah Ya albarkaci wannan jiha da masu basira, don haka akwai bukatar matasa su cusa kansu cikin sana’o’i na kwarai, don su dogara da kansu da ciyar da jihar gaba.

Yayi anfani da wannan dama yayi godiya wa matasan da suka ga dacewarsa suka karramashi, yana mai bada tabbacin cigaba da bada goyon baya wajen dabbaka manufofi da shirye shiryen gwamnatin a duk fadin wannan jiha.

Da yake tsokaci a wajen taron, Mataimakin Kakakin Majalisar dokokin jiha Hon. Babangida AbdulLahi, kira yayi ga sauran masu mukaman siyasa a jiha, suyi koyi da salon shugabanci irin na Comrade Danturaki, a fagen yi wa al’umma hidima.

Sauran manyan mutanen da suka halarci taron sun hada da Kwamishinar ilimi Hajia Jamila Muhammad Dahiru, Kwamishinan kiwon lafiya, Mukaddashiyar Mataimakiyar Shugabar mata ta jam’iyyar PDP ta kasa, da Hajia Maryam Garba Bage da saurans

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com