Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
AddiniLabaran Jiha
Trending

Kwalejin kasa da kasa ta Al-Huda dake Bauchi ta yaye Dalibai 147

A jawabin sa a wurin bikin yayewar, mai Martaba Sarkin Misau, Alhaji Ahmad Sulaiman, ya tuna cewa an bude Makarantar ta Al-Hudda ne a Shekara ta 2003 tareda Dalibai 180 da Malamai 5.

Kwalejin kasa da kasa ta Al-Hudda dake Bauchi, ta yaye Dalibai 147 daga ajujjuwan Haddahr Alqur’ani da Tarteel na Makarantar.

A jawabin sa a wurin bikin yayewar, mai Martaba Sarkin Misau, Alhaji Ahmad Sulaiman, ya tuna cewa an bude Makarantar ta Al-Hudda ne a Shekara ta 2003 tareda Dalibai 180 da Malamai 5, amma yanzu tana da Malamai sama da 30 da Dalibai wajen Dubu Daya.

Sarkin na Misau wanda ya samu wakilcin Hakimin kasar Hardawa Alhaji Abubakar Garba Lili, yayi kiran inganta Makarantun Islamiya a fadin Jihar Bauchi don samar da Al’umma tagari.

A nasa jawabin, mataimakin Shugaban Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi, Farfesa Ahmad Muhammad Abdul’azeez, wanda yake kuma shine shugaban taron, ya jaddada bukatar dake akwai, ta hada hannu wuri guda wajen inganta ilimin Islamiya.

Farfesa Ahmad Abdul’azeez, ya bayyana gamsuwa bisa irin gudumawar da Ma’aikatan gudanar da Makarantar ke bayarwa wajen cusawa Dalibai nagartaccen Ilimi da kyawawan dabi’un Musulunci, tare da yin kiran dorewar hakan.

HOTUNA DAGA WURIN TARON

 

Manyan baki masu jawabi a wurin taron, shugaban sashin nazarin Shari’ar Musulunci na Jami’ar Bayero dake Kano, Farfesa Mansur Isah Yelwa da Babban Sakataren Hukumar Jin Dadi da Walwalar Alhazai ta Jihar Bauchi, Imam Abdulrahman Ibrahim Idris, sun baiyana neman Ilimin addinin Musulunci da cewa wajibi ne ga kowanne Musulmi domin Susan yadda zasu bautawa Mahaliccin su kamar yadda yake kunshe cikin Alqur’ani mai Girmama.

Sun kuma yi kira ga iyaye dasu kara maida hankali Wajen koyawa ‘ya’yansu ilimin Addinin Islama don samun rabauta a Duniya da lahira.

Farfesa Mansur Isah Yelwa da Imam Abdulrahman Ibrahim Idris, sun taya Daliban da aka yaye murna, Musamman ma Tsoffin Daliban Makarantar bisa juriya da suka nuna a yayin koyon Ilimi, tare da yin kira a gare su da suyi kyakkyawan amfani da ilimin da suka samu wajen kyautata ibadar su.

A cikin jawabin godiya Amadadin Daliban da aka yaye, Alhaji Saleh Yakubu Ningi, ya godewa Allah bisa tsawaita Rayuwar su da har suka shaida Ranar yaye su amatsayin wadanda suka sauke Littafin Alqur’ani mai girma, tareda godewa Malaman Makarantar wajen sadaukar dakai, sai yayi Addu’ar, Allah ya saka musu da mafificin Alqur’ani.

Shima daya daga cikin Daliban da aka yaye daga bangaren Manya, Shugaban Asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi Farfesa Yusuf Jibrin Bara, ya bayyana neman Addinin Islama amatsayin garkuwar wajen kwantar da hankali da nutsuwa, sai yayi kira ga sauran Manyan Mutane da tashi haikan ba tareda la’akari da tsufa ba.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com