Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
LabaraiLabaran Jiha

KOTUN DAUKAKA KARA TA TABBATAR DA NASARAR SARKIN ALHAZAN BAUCHI

KOTUN DAUKAKA KARA TA TABBATAR DA NASARAR SARKIN ALHAZAN BAUCHI A MATSAYIN DAN MAJALISAR WAKILAI.

Wata Kotun daukaka kara dake zama a Abuja, ta tabbatar da nasarar Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar K/hukumar Bauchi Alh. Aminu Aliyu Garu, Sarkin alhazan Bauchi.

Da yake jawabi ga wakilinmu jim kadan bayan hukuncin kotun, Alh. Aminu Aliyu Garu ya bayyana godiyarsa ga Allah Madaukaki, bisa nasarar da yayi a zaben, wanda ya gudana ran 18 ga watan Maris na bana.

Dan Majalisan yayi anfani da wannan dama, ya roki sauran ‘yan Jam’iyyun siyasa, msamman Jam’iyyar APC, su hada hanu tare don ciyar da wannan jiha gaba.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com