Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
IlimiLabaran Kasa

KADDAMAR DA AYYUKA A JAMI’AR ATBU BAUCHI.

Jami’ar ATBU ta Bauchi tayi kira ga Gwamnatocin Tarayya da jiha su taimaka wa Cibiyoyin ilimi da bukatun kayan koyarwa, don cigaban kasa baki daya. Shugaban Jami’ar Prof. Muhammad Ahmad AbdulAziz ne yayi wannan kira, yayin kaddamar da manyan ayyuka guda 19 da aka aiwatar a cikin shekaru biyar, a matsayin wani bangare na hidimomin bikin yaye dalibai na Jami’ar da akayi a Mazaunin Jami’ar dake Gubi.

Shugaban Jami’ar, wanda Prof. Sani Usman Kunya ya wakilta, ya bayyana cewa manyan ayyuka guda 15 sun hada da azuzuwan karatu, dakin shan magani, dakin ajiye kayayyaki, dakin karatu, Ofisoshin malamai da sauransu da suke a ko’ina cikin matsugunan Jami’ar dake Gubi da Yelwa.

Da yake yaba wa Ma’aikatu, Sassa da Hukumomin Gwamnatin Tarayya, bisa gudumawar da suka bayar wajen tabbatar da ayyukan, Shugaban Jami’ar ya tabbatar da shirin Jami’ar na bada goyon baya da hadin kai ga dukkan gwamntoci a dukkan matakai, don cimma maradun samar da ilimi da aka sa a gaba.

Prof. Muhammad AbdulAziz yayi anfani da wannan dama, ya yaba wa Gwamnatin Jiha, bisa taimakon da ta baiwa Jami’ar ta ATBU, musamman a bangaren gina hanyar da ta kai zuwa matsugunin Jami’ar na Gubi da kuma kokarinta na ganin an kara inganta matsayin ilimi a wannan jiha.

Gwamna Bala Muhammad da takwaransa ya Jihar Katsina Dikko Radda ne suka kaddamar da ayyukan, sai kuma Masu martaba Sarakunan Bauchi, Katagum da Misau da sauran manyan baki da suka halarci bikin.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com