Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
IlimiLabaran Jiha

ILIMI ZAI CIGABA DA SAMUN FIFIKO A KARAMAR HUKUMAR GIADE

ILIMI ZAI CIGABA DA SAMUN FIFIKO A KARAMAR HUKUMAR GIADE FIYE DA KOWANNE SASHE.

Shugaban Kwamitin riko na K/hukumar Giade Alh. Usman Muhammad Sale yayi gargadin cewa, Majaliar K/hukumar ba zata lamunci duk wani yunkurin zagon kasa da wani zaiyi wa kokarin gwamnatin jiha na kara inganta sashen ilimi ba, domin ilimi har gobe shi ne kan gaba a wajen gwamantin jiha.

Shugaban K/hukumar, wanda yayi wannan gargadi, yayin gangamin daukan yara a matakaranta na zangon karatun 2023/2024 a Kauyen Uzum dake K/hukumar, yace wajibi akan iyaye a yankin, su tabbatar sun tura ‘ya’yansu zuwa makaranta.

Da yake jawabi tun farko, Sakataren ilimi a K/hukumar Malam Sulaiman Baba, yace gangamin wannan shekara, na burin tabbatar da ganin an kakkabe batun yaran da basa zuwa makaranta ne a wannan jiha, yana mai cewa kokarin da Gwamnan jiha keyi ta wannan fiska, kamata yayi kowa yayi koyi dashi.

Yayi gargadin cewa Hukumar kula da ilimi ba zata yarda da kin zuwa bakin aiki da malamai keyi ba, musamman wadanda aka tura zuwa yankunan karkara, wadanda galibi basa zuwa makarantun da aka turasu, yana mai karawa da cewa, akwai wani kwamiti dake aiki, ba dare ba rana, don tabbatar da cewa, malamai sun shiga aji don bada karatu.

Cikin tsokacinsa irin Uban kasa, Hakimin kasar Giade Alh. Muhammadu Sabo AbdulQadir, wanda yayi jawabi ta bakin Hakimin kasar Jawo, Alh. Aliyu Umar, yace zasu bar kofofinsu a bude a kowane lokaci, kuma zasu cigaba da mara baya wa manufofi da shirye shiryen gwamnati, don kara inganta rayuwar al’umma gaba daya.

A cewarsa, sun dade suna jan hankalin al’ummarsu, don tabbatar da cewa dukkan yaran da suka isa zuwa makaranta an musu rijista a makarantu, yana mai cewa ilimi shi ne mabudin cigaban al’umma.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com