Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
IlimiLabaran Jiha

Hukumar SUBEB ta Jihar Bauchi tayi alkawarin tabbatar da gudanar sashen ilimi yadda ya kamata a jihar.

Hukumar samar da ilimi bai-daya ta jihar Bauchi – SUBEB, tayi alkawarin tabbatar da gudanar sashen ilimi yadda ya kamata a jihar.

Babban Sakataren Hukumar Alhaji Sale Yakubu Ningi ne ya sanar da hakan ga manema labarai, bayan da ya kare kasafin kudin Hukumar na shekarar badi, a gaban Kwamitin ilimi na Majalisar dokokin jihar Bauchi

Yace Hukumar ta tsara wasu shirye shirye a cikin kasafin, don tabbatar da samun yanayi mai kyau na koyo da koyawa, ga malamai da dalibai

Alh. Sale Ningi yace SUBEB zata samar da isassun kayan koyarwa a makarantun primary a duk fadin jihar, baya ga gina sabbin azuzuwa da gyara wadanda suka lalace, don daukaka darajar ilimi a jihar.

A wani labarin kuma, Shugaban Kwamitin tsaro na Majalisar dokokin jihar Bauchi Hon. Garba Lawal, yayi kiran samun fahimta, tsakanin al’ummu da addinai, don dorewar zaman lafiya da fahimtar juna a jihar. Yayi wannan kira ne, cikin wata hira da yayi da manema labarai a Majalisar dokokin jihar Bauchi. A cewarsa, babu wani cigaba mai ma’ana da za’a samu a yanayi na rudani. Don haka akwai bukatar al’ummar jihar ta Bauchi ta zama mai hakuri da juna, ba tare da la’akari da banbancin siyasa da addini ba. Sannan ya jinjina wa ‘yan Majalisar, bisa kyakkyawar dangantakar aiki dake wanzuwa tsakanin bangaren Majalisar da na Zartaswa.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com