Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
IlimiLabaraiLabaran Jiha

HUKUMAR GUDANARWAR JAMI’AR ATBU TA BAUCHI FITAR DA SABON TSARIN BIYAN KUDIN MAKARANTA

HUKUMAR GUDANAR DA JAMI’AR ATBU TA BAUCHI TA FITAR DA SABON TSARIN BIYAN KUDIN MAKARANTA NA TSOFFI DA SABBIN DALIBAN JAMI’AR.

Hukumar gudanarwar Jami’ar ATBU ta Bauchi, ta fitar da sabon tsarin yin rijista ga tsoffi da sabbin daliban Jami’ar.

Cikin wata sanarwa dauke da sa hanun Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na Jami’ar Malam Zailani Bappah, yace wannan sanarwar, ta shafe dukkan bayanai da cece-kuce game da sabon tsarin biyan rijistar na kwanakin baya.

A cewar sanarwar, sabon tsarin ya kunshi cewa sabbin dalibai masu nazarin aikin likitanci – MBBS zasu biya kudi mafi yawa na naira dubu 150 ne, a yayin da kudi mafi karanci da tsoffin dalibai a sauran kwasakwasai, amma banda masu nazarin aikin likitanci, zasu biya naira dubu 69 da 700.

Sanarwar ta bayyana cewa, sabon dalibi dan kasar waje, zai biya naira dubu 230, shi kuma tsohon dalibi dan kasar waje, zai biya naira dubu 183.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com