Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran JihaLafiya

Harkar Lafiya: An bukaci ma’aikatan kiwon lafiya su kara zage damtse

Rabi'u Ishaq Mohammed

An bukaci ma’aikatan lafiya a Jihar Bauchi su kara sadaukar da kansu bisa aikinsu, don daga darajar aikin kula da lafiya a daukacin Jihar baki daya. Shugaban Kwamitin kula da lafiya da ma’aikata na Majalisar Dokokin Jihar Hon Lawal Dauda ne yayi wannan kira yayin wata ziyarar aiki da ya kai wasu Cibiyoyin kula da lafiya a Bauchi.

Hon. Dauda ya kuma bukaci ma’aikatan lafiyan suyi tsayuwar gwamen jaki akan ka’idojin aikinsu, sannan su tabbata sun kasance masu da’a, don cigaban sashen kula da lafiya a duk fadin jihar ta Bauchi.

Shugaban Kwamitin ya bayyana cewa maksudin ziyarar aikin nasa, shi ne gano matsayin da asibitocin suke, karfafa gwiwar ma’aikata da sauran muhimman bukatu, da nufin samar da mafita ta dindindin ga matsalolin da aikin kula da lafiya ke fiskanta a JIhar Bauchi. Yana mai basu tabbacin cewa Kwamitin zai gabatar da shawarwari da rahoto da zasuyi wa asibitocin dadi, don samun kyautatuwar yanayin aikinsu.

Cibiyoyin kula da lafiyan da Kwamitin ya ziyarta, sun hada da Cibiyoyin kula da lafiya na Alangawari a Karamar Hukumar Gamawa, Hardawa a Karamar Hukumar Misau, Kari da Sade a Karamar Hukumar Darazau, da Asibitin haihuwa na Azare a Karamar Hukumar Katagum da sauransu.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com