Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Lafiya

Gwamnatin jihar Bauchi zata gina madatsun ruwa guda 30 a duk fadin K/hukumomi 20 na jihar.

Gwamnatin jihar Bauchi tace zata gina madatsun ruwa guda 30 a duk fadin K/hukumomi 20 na jihar.

Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Alh. AbdurRazzaq Nuhu Zaki ne ya sanar da haka, bayan ya kare kasafin kudin Ma’aikatar na shekarar 2024, a gaban Majalisar dokokin jihar. Yace baya ga haka kuma, akwai shirin samar da ruwan sha mai tsabta ga al’ummar jihar baki daya.

Kwamishinan yace nan gaba kadan za’a kaddamar da manyan ayyukan raya kasa a garuruwan jihar, domin wadanda aka fara a Garin Futuk, ya kusa kammala.

Kazalika, Ma’aikatar ma’adinai ta jihar, tayi alkawarin habaka ayyukan tonon ma’adinan da Allah Ya albarkaci jihar dasu.

Kwamishinan Ma’aikatar Mal. Maiwada Bello ne ya furta haka, lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin kula da ma’adinai na Majalisar dokokin jihar, don kare kasafin kudin Ma’aikatar, na shekara mai zuwa.

Yace Ma’aikatar ta shata wasu matakai, don kakkafa Cibiyoyin tonon ma’adinai a duk fadin jihar, a kokarinta N kara yawan kudaden shiga da samar da aikin yi.

Alh. Maiwada Bello ya bayyana cewa, Ma’aikatar ta ware naira miliyan dubu guda a cikin tsarin kasafin, don gina sabuwar Makarantar nazari albarkatun man fetur da iskar gas ta dindindin a Alkaleri, don ta fara gudanar da harkokin karatu gadan-gadan.

Kwamishinan yace kuma an sanya batun sabbin kayan aiki, a cikin kasafin kudin na shekara mai zuwa, don bincike da tono ma’adinai dake can karkashin kasa.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com