Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Jiha

gwamnatin jihar Bauchi ta tsara wasu dabarun yaki da sauyin yanayi ta hanyar dasa itatuwa

Kwamishinan Ma’aikatar gidaje da kula da muhalli ta jihar Bauchi Hon. Danlami Ahmed Kawule, yace gwamnatin jihar ta tsara wasu dabarun yaki da sauyin yanayi, ta hanyar dasa itatuwa.

Danlami Kawule, ya bayyana hakan ne, bayan da ya kare kasafin kudin Ma’aikatar na shekara mai kamawa a gaban Majalisar dokokin jihar. Yana mai bayyana cewar har yanzu dashen itatuwa ne babban malamin hana tabarbarewar muhalli da kwararo war hamada da sauran matsalolin sauyin yanayi.

A halin da ake ciki, Ma’aikatar matasa da wasanni ta jahar Bauchi, tace ana kan kokarin fara ginin Kwalejin koyar da wasanni a Bauchi.

Da yake jawabi ga manema labarai, bayan kare kasafin kudin Ma’aikatar na shekara 2024, Kwamishinan Maaikatar Salisu Muhammad Gamawa, yace muhimman bangarori shida dake kunshe cikin kundin Maaikatar, maksudinsu shine maida wasanni su zama jari mai riba, ba nishadi kadai ba.

Salisu Gamawa yace Ma’aikatar, tayi shirin karfafa wa matasa gwiwa da sauran shirye shiryen da zasu kara kyautata rayuwar matasan jihar.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com