Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Jiha

GWAMNATIN JIHAR BAUCHI TA GWANGWAJE HUKUMAR ‘YAN KWANA-KWANA TA JIHA DA KAYAN AIKI IRIN NA ZAMANI.

A yunkurinta na shawo kan karuwar aukuwar gobara a yankunan karkarar jihar Bauchi, Gwamnatin Jihar ta iza kaimi wa Hukumar ‘yan Kwana-kwana ta jihar da kayan kashe gobara na zamani, don samun sukunin kashe gobara da ceto rayuka da dukiya yadda ya kamata.

A lokacin da yake duba kayayyakin a wannan laraba 10 ga watan Janairun 2024 a Hedkwatar Hukumar dake Bauchi, Kwamishinan Ayyuka da Sufuri na Jihar Alh. Ibrahim Gambo Galadima, yace maksudin ziyarar ita ce tantance halin da motocin kashe gobarar ke ciki, yana mai nanata shirin Gwamna Bala Muhammad, na tabbatar da kariya ga lafiya da dukiyar al’umma.

Ya bayyana cewa Gwamnati ta sayo sabbin motocin kashe gobara guda hudu, sannan ta gyara wasu guda hudu, da nufin magance matsalolin rashin kayan aikin kashe gobara, don taimaka wa Jami’an Hukumar a Majalisun Kananan Hukumomi.

Alh. Ibrahim Galadima ya bayyana cewa Gwamna Bala Muhammad ya amince da rarraba sabbin motocin kashe gobarar zuwa Kananan Tashoshin Hukumar dake Kananan Hukumomin Ningi, Alkaleri, Bauchi da Zaki, motocin da aka gyara kuma za’a turasu zuwa kananan tashoshin ‘yan kwana-kwana dake Kananan Hukumomin Toro, Dass, Darazau da Misau.

Tun farko cikin jawabinsa, Daraktan Hukumar na Jihar Bauchi Injiniya Bala Abubakar Garba, ya yaba wa Kwamishinan, bisa ziyarar ba-zata da ya kai, sannan ya gode wa gwamnatin jiha da ta karfafi Hukumar da sabbin kayan aiki. Sannan yayi anfani da wannan kafa, ya gargadi mutane dake anfani da kayayyaki masu hadari, wadanda ka iya haddasa gobara, wanda hakan ke haifar da matsin lamba wa Hukumar ‘yan kwana-kwana ta jiha.

Kwamishinan ya samu rakiyar Babban Sakataren Ma’aikatar Alh. Abubakar Usman Misau da Daraktan kudi da Asusun Ma’aikatar Alh. Haladu Akuyam, a ziyarar da ya kai.

Motocin
Ma’aikatar ayyuka da sufuri

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com