Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Jiha

GWAMNATIN JIHAR BAUCHI NA SHIRIN SAKE BULLO DA SHIRIN “GYARA KAYANKA

Gwamnatin Jihar Bauchi tace tana kokarin ganin ta bullo da wasu dabarun sake kaddamar da Shirin gyaran halin al’umma, da nufin sauya munanan tunanin da al’umma ke dasu a wannan jiha.

Kwamishinan harkokin addini da kyautata halayyar jama’a na Jiha Alh. Yakubu Ibrahim Hamza ne ya bayyana haka, cikin wata zantawa da manema labarai, jim-kadan bayan wata ganawa da yayi da masu ruwa da tsaki a Bauchi.

Alh. Yakubu Hamza ya bayyana cewa daga cikin dabarun akwai janyo muhimman masu ruwa da tsaki, wadanda ke da masaniya game da Shirin ‘Gyara Kayanka’ da aka taba yi a baya, don su bada gudumawa wajen ganin Shirin ya tabbata.

Kwamishinan yace malamai da sarakuna da ma Shugabannin al’umma, zasu kasance bangaren masu ruwa da tsakin, yana mai cwea, za’a kafa wani Kwamiti, don tabbatar da ganin an aiwatar da shirin yadda ya kamata.

Taron, ya samu halartan Kwamishinonin harkokin jin-kai, Kyautata rayuwar matasa da wasanni, yada labarai, ilimi mai zurfi, harkokin ilimi, harkokin K/hukumomi da masarautu da sauransu.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com