Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Ilimi

Gwamnatin Jiha ta dauki Kudirin Sanya farin ciki ga Daliban kwana na Jihar Bauchi

Kwamishinar ilimi ta jiha Hajia Jamila Dahiru, ta dauki matakin kan-da-garki, don tabbatar da ganin cewa daliban dake makarantun kwana sun samu cikakkiyar kulawa ta fiskar lafiya da wadataccen abinci.
Cikin wani ran-gadi na kwanakinnan, ta umurci hanzarta raba kayayyakin abinci daban-daban, tana mai jaddada muhimmancin samun abinci mai gina jiki ga dalibai, don samun lafiya da nasara a karatunsu.
Kayayyakin abincin da aka raba sun hada da gero, shinkafa, wake, madara, sukari, ganyen shayin lipton, man ja, man gyada da cornflakes.
Kwamishinar ta nanata bukatar sanya ido kan tabbtar da ganin dukkan daliban sun samu isashshen abinci, tana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da hau wajen karkatar da kayan abincin, zai dandana kudarsa.
Da take bayyana godiyarta ga Gwamna Bala Muhammad, Kwamishinar ta gamsu da kwarin niyyarsa game da sha’anin ilimi, bisa yadda ya samar da wadataccen abinci ga daliban.
Umurnin Kwamishinar, wata alama ce mai karfi dake tabbatar da cewa daliban dake makarantun kwana sun samu damar cin abinci mai inganci, don taimaka wa jikinsu da ruhinsu, wajen fiskantar karatunsu yadda ya kamata.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com