Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran JihaTsaro

Gwamnati Jihar Bauchi Ta Kaddamar da makon tunawa da ‘yan Mazan Jiya da sama da Nera Miliyan 10

Da Dumi Dumi:

Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad ya Kaddamar da makon tunawa da ‘yan Mazan Jiya da kimanin kudi sama da Nera Miliyan 10, a yau Alhamis a Shirye shiryen bikin ranar tunawa da gudumawar ‘yan Mazan Jiya dake gudana a Ranar 15 ga Watan Janairun 2024.

Gwamnan ya yi kira ga sauran ‘yan kasuwa da masu hannu da shuni wajen taimakawa iyalan wadanda suka Tabbatar da hadin kan Nigeria.

Cikin jawabinsa Shugaban Kungiyar Tsoffin sojojin Nigeria reshen Jihar Bauchi Idris Danjuma Ningi, yace Gwamnatin Bala Muhammad ta gina musu sabon Ofishi, wanda Kungiyar take nema sama da shekaru 40 da suka wuce.

Cikin sakon ta na fatan Alkhairi ga Gwamnatin Jihar Bauchi, Shugabar Kungiyar Matan Tsoffin Sojojin Nigeria ta kasa, Ambassador Fatima Idris Danjuma, tayi kira ga sauran Gwamnanonin Nigeria da yin koyi da Gwamnan Jihar Bauchi wajen taimakawa iyalan Tsoffin sojoji a fadin Jihohin su.

Sai ta bukaci Gwamna Bala da ya taimakawa Kungiyar da Abun hawa don sauwake Lammuran zirga zirgar Kungiyar.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com