Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
IlimiLabaran Jiha

Gwamnan Jihar Bauchi ya ware naira miliyan 396 da 963, don biyan kudin jarabawar NECO, da WAEC,

Gwamnan Jiha ya ware naira miliyan 396 da 963, don biyan kudin jarabawar da ake shiryawa daga waje ta Hukumomin shirya jarabawa na NECO, WAEC, NBAIS da JAMB, wa dalibai dubu 14 da 170 daga dukkan fadin wannan jiha, a shekarar karatu ta 2023/2024.
Cikin wata sanarwa dauke da sa hanun Jami’in yada labarai na Ma’aikatar Ilimi ta jiha Mal. Jalaluddeen Usman, yace wannan karimci, ya dace da manufar Gwamna Bala Muhammad na taimaka wa sashen ilimi, a kokarinsa na daga darajar sashen a wannan jiha.
Sanarwar tace ba kamar yadda lamarin yake a gwamnatocin baya ba, inda ake jinkirta biyan irin wannan kudi, Gwamna Bala Muhammad ya biya wannan, kuma ya biya bashin naira sama da miliyan 800 na jarabawar da akayi tun daga shekarar 2020, da nufin kara inganta matakan koyon karatu ga yara ‘yan makaranta.
Ta kara da cewa kokarin gwamnati na biyan kudin rijistar jarabawar share fagen shiga jami’a – JAMB, ga dalibai dubu daya da 542 da suka rage a yayin jarabawar gwajin kwazo, wani muhimmin yunkuri ne na zaburar da sauran dalibai su kara kokari akan harkokin karatunsu
Ma’aikatar ilimi ta jiha da sauran masu ruwa da tsaki da take mu’amala dasu, sun yaba da yunkurin na Gwamna Bala Muhammad, saboda hangen nesansa, tsayin dakansa da kuma shugabanci na kwarai da yake nunawa, wjaen tallafa wa cigaban ilimi a wannan jiha.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com