Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
IlimiLabaran Jiha

Gwamnan Jihar Bauchi ya taya murna wa Mahukuntan Jami’ar ATBU ta Bauchi, bisa yaye rukunin farko na dalibanta.

Gwamna Bala Muhammad na Jihar Bauchi ya taya murna wa Mahukuntan Jami’ar ATBU ta Bauchi, bisa yaye rukunin farko na dalibanta da suka karanci aikin likita.

Da yake jawabi a yayin bikin yaye daliban Jami’ar karo na 26, 27, 28 da 29 a hade, wanda ya gudana a mazaunin Jami’ar dake Gubi a Bauchi, Gwamnan yace saboda gamsuwa da wannan cigaba, gwamnatin jiha zata dauki daliban aiki, a wani yunkuri na magance karancin likitoci a Cibiyoyin kula da lafiya dake wannan jiha.
Ta bakin Wakilinsa, kuma Mataimakinsa Rt Hon. Muhammad Auwal Jatau, Gwamna Bala yace Jami’ar ATBU ta Bauchi, ta kasance wata madogarar ilimi da kirkire-kirkire, inda tayi zarra ta kere sa’o’inta a kasar nan.

Ya bayyana cewa jajircewar Jami’ar, a bangaren kwarewa da samar da ilimi a bayyane yake, a manhajojinta na tsare-tsaren karatu da sukayi fice, da sadaukan tsangayoyinta da kuma kayan koyarwanta irin na zamani masu inganci, yana mai karawa da cewa, bisa irin namijin kokarin da take dauka a bangaren samar da ilimi, Jami’ar ATBU ta Bauchi, ta kyankyashe Shugabanni da suka bada gagarumar gudumawa a fannoni daban daban na rayuwar al’umma.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta cigaba da bada gudumawa a bangaren ilimi, wadanda sukayi naso a manufofi da shirye shiryen da aka aiwatar zuwa yanzu, yana mai karawa da cewa a yanzu da aka fara aiwatar da sabbin manufofin, musamman ma wajen kyautata anfani da fasaha da matakan sanya ido, ta samu nasarar rage asara da ayyukan cin hanci da rashwa a tsarin ilimi.

Gwamna Bala Muhammad ya nanata shirin gwamnatinsa na cigaba da bada kudade masu tsoka a sashen ilimi, samar da yanayi mai kyau ga Cibiyoyin ilimi ta yadda zasuyi tasiri mai kyau, ya kuma bada tabbacin cewa gwamnatinsa ba zata gajiya ba, sai ta ga dukkan ‘yan kasa da suka cancanta a wannan jiha sun samu damar samun ilimi mai nagarta, don karfafa wa kokarin Jami’ar na haifar da dalibai masu kwazo, wadanda zasu jagoranci al’umma zuwa ga tudun mun-tsira a nan gaba.

Don haka ya bayyana tsantsar godiyarsa ga kowane ma’abocin Jami’ar ta ATBU, bisa jajircewasu wajen tabbatar da ingancin harkokin karatu a Jami’ar, kuma yayi alkawarin cigaba da yaukaka dangantaka tsakanin Jami’ar da Gwamnatin Jiha.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com