Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Addini

GWAMNA BALA YAYI BUDA-BAKI DA MALAMAI

Gwamna Bala Muhammad ya jinjina wa malaman addini a wannan jiha, bisa fahimtar juna dake tsakanin mabiya addinan musulunci da kirista a wannan jiha. Ya bayyana haka ne, yayin buda-baki da yayi da malamai da shugabannin addinan biyu daga ko’ina a fadin wannan jiha, wanda ya gudana a Sansanin alhazai na Sultan Sa’ad Abubakar ran laraba 13 ga watan nan na Maris.

Yayin liyafar buda-bakin, wanda ya samu halartar malaman addini, shugabanni da ‘yan siyasa da ‘yan boko, Gwamna Bala ya bayyana jin dadinsa da yadda al’ummar musulmin wannan jiha ke nuna goyon baya ga gwamnatinsa, kuma ya bukaci su dore akan haka, don cigaban zaman lafiya, girmamawa da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai a wannan jiha.

Gwamnan ya nanata cewa wannan jiha tana more zaman lafiya da kwanciyar hankali, har ta zama abin misali a kasar nan, yana mai kira ga shugabannin musulmi suyi anfani da wannan dama na watan Ramadan, wajen yin addu’o’i samun dacewa daga Allah Madaukaki da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Bauchi da Nigeria baki daya.

Yayi fatan cewa dama ta musamman da watan Ramadan ya bayar, zai kara zurfafa fahimtar juna a kasar nan, ya kuma zaburar da ‘yan kasa suyi aiki tukuru wajen gina kasa da nuna kauna ga mabukata. Sannan yayi godiya wa bakinsa mahalarta liyafar buda-bakin, wadanda yace suna da karfafa hadin kan kasar nan a zukatan kowannensu.

Liyafar buda-bakin ta samu halartan mashhuran malaman addinin musulunci, irin su Prof. Sani Umar Rijiyar Lemo, Shugaban Kungiyar kiristoci ta Nigeria – CAN Reshen jiha, Jagoran Kungiyar Izala ta JIBWIS Reshen jiha Prof. Zubairu Abubakar Madaki da Wakilin Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com