Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran JihaTaskar Labarai

Gwamna Bala yayi Alkawarin inganta tsari da nagartar aikin gwamnatin jihar Bauchi.

 

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed, ya ayyana shirin gwamnatinsa na yin aiki tare da Ofishin shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, wajen kare inganta tsari da nagartar aikin gwamnatin jihar Bauchi.

Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad na Jihar Bauchi

Gwamnan ya bayyana hakan ne, yayin bude babban taron Majalisar kula da ma’aikatun gwamnati ta kasa – NCE karo na 45,wanda gwamnatin jihar Bauchi ke daukan nauyin bakuncinsa a masaukin baki na Barikin soja dake Bauchi. Yana mai jinjina wa mambobin Majalisar, bisa namijin aiki da tattaunawa da sukeyi, don samo hanyar da tafi dacewa abi, don daga darajar aikin gwamnati, a matakin jiha da tarayya.

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed, yace aikin gwamnati, a matsayinsa na bangaren da aka dora wa hakkin aiwatar da shirye shirye da manufofin gwamnati, ya dade yana samun kulawar da yake bukata a wajen gwamnatinsa, tun bayan da ya amshi ragamar iko a shekarar 2019, kuma ya yunkura sosai wajen kyautata rayuwar ma’aikata da inganta musu yanayin aiki, don haka ta cimma ruwa.

Gwamnan yace a kokarinta na magance matsalar karancin ma’aikata, gwamnatinsa ta amince da daukar sabbin ma’aikata a muhimman sassa ma’aikatun gwamnati da kakkafa Cibiyoyin koyar da sana’o’i, don horas da matasa da mata fasahohi da kirkire-kirkire, don su samu damar dogaro da kansu yadda ya kamata.

A nata bangaren, Shugabar ma’aikatan Gwamnatin tarayya Dr. Folaahade Yemi-Esan, tace taron Majalisar, yazo a daidai lokacin da bukatar tsarin aiki gwamnati mai nagarta ke kara karuwa, don haka akwai bukatar masu ruwa da tsaki su kara hada karfi da karfe, don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu a wannan bangaren.

Shugabar Ma’aikatar Gwamnatin Tarayya Dr Folaahade Yemi-Esan

Tace Kundin tsari da ka’idojin aikin gwamnati da akayi wa bita, ya bijiro da sabbin batutuwa, wadanda suka hada da tsawaita kwanakin hutun haihuwa, daga makonni 16 zuwa kwanaki 112, bullo da hutun kwanaki 14 ga mahaifi, karin kudin alawus na barin aiki zuwa kashi 25 daga cikin dari da kuma bullo da manufar wa’adi wa manyan Sakatarori da Daraktoci, da nufin magance matsalar kasancewa jirgin dankaro da kuma tabbatar da ganin ma’aikata sun samu cigaba zuwa matsayi na gaba.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com