Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
AddiniIlimi

GWAMNA BALA YA YABA WA KWAMITIN MUSABAKAR AL-QURANI NA JIHAR BAUCHI.

Daga Yahuza Yahaya Doka:

Gwmana Bala Muhammad na jihar Bauchi, ya cira hula wa Kwamitin musabakar al-Qurani mai girma na jihar, bisa jajircewa da yayi wajen cire wa jihar kitse a wuta a yayin musabakar al-Qurani mai girma ta kasa da aka gudanar a karshen shekarar da ta gabata a Damaturu, Fadar jihar Yobe.

Gwamnan, wanda yayi yabon a lokacin da ya marabci mambobin Kwamitin a Gidan Gwamnatin jihar Bauchi, yace Kwamitin yayi abin yabo, wanda har abada za’a rika tunawa dashi

Gwamna Bala Mohammad yace dalibin da ya zama Gwarzo a wajen musabakar, wanda kuma dan asalin jihar Bauchi ne, shi ne zai wakilci Kasar nan a musabakar ta duniya baki daya, yana mai bayyanashi a matsayin abin alfahari ga gwamnati, al’ummar jihar da kasa baki daya.

Gwamnan ya sanar da cewar za’a karrama wadanda suka zama gwaraza a musabakar ta kasa da aka gudanar a Jihar Yobe, da nufin yin musu kaimi, su kara kwazo.

Tun farko, Shugaban Kwamitin musabakar karatun al-Qurani na jihar Bauchi Imam Hassan Usman Zango, wanda ya taya Gwamnan murna bisa nasara a Kotun koli, yayi masa godiya, bisa goyon bayan da ya baiwa Kwamitin, kafin da yayin gudanar da musabakar, a matakin jiha da kasa baki daya.

Imam Hassan Zango, yayi amfani da wannan damar, yayi kira ga Gwamnan da ya kara jan damarar aiwatar da karin ayyukan kyautata rayuwar al’ummar jihar Bauchi.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com