Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Jiha

Gwamna Bala ya yaba da Shugabancin Kungiyar ‘yan Jarida wajen aiki bisa kwarewa

Daga Muslim Lawal:

Gwamna Bala Mohammed yace ya ji dadi da irin kyakkyawan shugabancin da Majalisar Kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya – NUJ Reshen Jihar Bauchi ke samarwa, ta hanyar tabbatar da kwarewa, duk da dinbin matsalolin da ake fama dasu a sha’anin aikin jaridan.

Ya zuwa yanzu, yayi alkawarin cika dukkan alkawarorin da gwamnatinsa tayi a sashen, don tabbatar da cikakken jin dadin yanayin aikin ‘yan jaridan, tare da samar musu isassun kayan aiki na zamani.

Gwamnan na bayyana hakan ne, lokacin da ya marabci shugabannin Kungiyar ta NUJ da takwararta ta Cibiyar hulda da jama’a ta kasa – NIPR, wadanda suka je tayashi murnar nasara da ya samu a Kotun koli.

Gwamnan, wanda ya bayyana jin dadi da ziyarar, ya bayyana cewar yana sane da alkawuran da yayi wa kungiyoyin, cikinsu har da batun gyaran Sakatariyar Kungiyar NUJ ta jihar Bauchi. Yana mai kiran dorewar kokarin da suke yi, musamman a bangaren yayata muhimman ayyukan kyautata rayuwar al’ummar jihar Bauchi.

Tun farko, Shugaban kungiyar NUJ ta jihar Bauchi Comrade Umar Sa’idu, wanda ya shaida damuwa da Gwamnan yayi da yanayin rayuwar ‘yan jarida ma’aikata da wadanda suka yi ritaya, ya nanata cewa gyaran Sakatariyar NUJ ta jihar, zai samar da yanayin aiki mai kyau wa’ yan jaridan.

Ya taya Gwamnan murna, bisa nasarar da yayi a Kotu, kuma ya bukaceshi da ya kara karfafa nasarorin da gwamnatinsa ta cimma zuwa yanzu.

A nasa bangaren, Shugaban Cibiyar NIPR a jihar Bauchi Rabi’u Wada, ya bayyana cewar tuni Cibiyar take aiki tare da Gwamnan, don ganin ya cimma nasarar aiwatar da Shirin bunkasa jihar Bauchi.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com