Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Jiha

Gwamna Bala ya ce Shugabannin Kungiyar Kwallon kafa ta Wikki sun gagara tabuka komai

Daga Muslim Lawal:

Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi, yace shugabannin Kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist da suka gabata, sun gaza sauke nauyin da aka dora musu, na kyautata rawar kungiyar a filin wasa.

Sakamakon haka ne Gwamnan ya tabbatar da goyon bayansa wa Kwamitin rikon kwaryar Kungiyar, da nufin maidata sahun zakakurai a kaka’ar gasar ta gaba.

Ya bayyana hakan ne, lokacin da ya marabci Kwamitin rikon kwaryar Kungiyar da sauran Hukumomin dake karkashin Ma’aikatar kyautata rayuwar matasa da wasanni, karkashin jagorancin Kwamishina Muhammad Salis Gamawa, wadanda suka kai wa Gwamnan ziyarar tayin murnar nasarar da yayi a Kotun koli. Yace Kungiyar Wikki Rourist, har yau tana cikin muhimman bangarorin da yake baiwa fifiko, kuma zai cigaba da yin hakan.

Gwamnan ya yaba da rawar gani da Kungiyar ta taka zuwa yanzu a gasanni na kasa, kuma ya sha alwashin tabbatar da ganin ta samu nasarar haurawa zuwa mataki na gaba.
Tun farko, cikin jawabin Kwamshinan matasa da wasannin Muhammad Salis Gamawa, yace maksudin ziyarar, ita ce tayin murna ga Gwamna, bisa nasarar da yayi a Kotun koli

Yace har abada, Ma’aikatar zata cigaba da yin godiya wa Gwamnan, bisa goyon bayan da yake baiwa shirye shiryenta, yana mai bada tabbacin baiwa marada kunya.

Wani Dan Kwamitin rikon kwaryar Kungiyar Umar Sa’idu, cikin wani takaitaccen jawabi, yayi godiya wa Gwamnan, bisa ya maida Kungiyar kwallon kafa ta Wikki, a matsayin wacce yake baiwa fifiko.

Lokacin da yake taya Gwamnan murnar nasara a Kotun koli, Madugun Kungiyar Muhammadu Idris Guda, yayi alkawarin’ yan wasan Kungiyar zasu kara azama, har sai haka ta cimma ruwa.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com