Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Kasuwanci

Gwamna Bala ya amince da bada naira miliyan 500, don samun nasarar gudanar da kasuwar baje kolin Arewa maso Gabas

Kwamishinan Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu ta jihar Bauchi Alh. Mahmud Baba Ma’aji, yace shirye shirye sunyi nisa, wajen daukar nauyin bakuncin bikin baje koli kayan da ake sarrafawa a cikin na Shiyyar Arewa maso gabas, a wannan jihar.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne cikin wata hira da yayi da manema labarai a Majalisar dokokin jihar Bauchi, bayan ya kammala kare tsarin kasafin kudin Ma’aikatar na shekara mai kamawa.

Yace tuni ma Gwamna Bala AbdulQadir Muhammad ya amince da bada naira miliyan 500, don samun nasarar gudanar da kasuwar baje kolin. A cewarsa, hakan, zai kara inganta harkokin tattalin arzikin wannan jiha.

Da yake maida jawabi, Shugaban Kwamitin Ciniki da Masana’antu na Majalisar, Hong. Sale Zakariyya, mai wakiltar Mazabar Azare/Madangala, yayi alkawarin yin aiki tare da Ma’aikatar, don tabbatar da ganin cewa, kudaden da aka ware mata, an batar dasu bisa gaskiya

A halin da ake ciki, Gwamnatin jihar Bauchi, da ware wa Ma’aikatar ilimi mai zurfi da hade kan shiyya ta jiha, naira miliyan dubu biyu da miliyan 900, cikin tsarin kasafin kudin badi.

Kwamishinar Ma’aikatar Mrs. Lydia Tsammani ce ta sanar da hakan, lokacin da take kare kasafin kudin Ma’aikatar na shekarar 2024,a gaban Kwamitin ilimi na Majalisar

Tace an dora wa Ma’aikatar alhakin samar da gine-gine da kayan aiki daga cikin kasafin, a sabuwar Kwalejin ilimin kere-kere da aka kafa a Dass da irinta ta nazarin harkokin mulki da aka kafa a Ningi.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com