Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
IlimiLabaran Jiha

Gwamna Bala Muhammad yace Babban burin gwamnatinsa, shi ne maido da martabar ilimi a makarantun gwamnatin jiha da ya gushe, ta hanyar magance daukacin matsalar karancin ma’aikata a sashen.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da yake bude babban taron koli na ini biyu kan sha’anin ilimi, wanda aka yi wa taken “Shiri don gaba: Inganta hanyoyin samun nagartaccen ilimi a Jihar Bauchi”, wanda ya gudana a Sansanin alhazai na Sultan Sa’ad Abubakar na uku dake Bauchi.

Gwamna Bala ya bayyana cewa taron kolin kan ilimi na jiha, ya ta’allaka ne kacokam, kan maganace batutuwan da suka takaita da sashen ilimi na wannan jiha, cikinsu har da yawan yaran da basa zuwa makarantun boko, inda suke zaune da tasirin da hakan keyi akan ilimi, sakamakon matsaloli daban daban.

Yace taron zai bidi sa hanun masu ruwa da tsaki sosai, ta hanyar wayar musu da kai da bidar gudumawarsu, a kokarin kara inganta sashen ilimi. Yana mai nanata shirin gwamnatinsa na inganta rayuwar al’umma da yin kaimi wa sha’anin cigaban zamantakewa da tattalin arzikin jiha, ta hanyar samar da ilimi mai nagarta wa yara da matasa, wadanda zasu kasance mutanen kwarai da shugabanni a gobe.

Gwamnan yace gwamnatinsa ta kara yawan kasafin kudi wa sashen ilimi, kuma ya kara da cewa gwamnatinsa ta yunkura, wajen tabbatar da ganin kwasakwasan da manyan Cibiyoyin ilimin wannan jiha ke bayarwa, sun samu tantancewa daga Hukumomin da lamarin ya shafa.

Yace a nata bangaren, Gwamnatin jiha ta gyara tsayuwar Ma’aikatar ilimi, don tinkarar matsalolin sabon karni, ta hanyar anfani da fasahar sadarwar zamani – ICT, wanda ya hada da fitar da sakamakon jarabawa, daukar dalibai, biyan kudaden karin ilimi da sauran muhimman batutuwa ta internet, wanda hakan ya kara tabbatar da kwatanta gaskiya, inganta hanyoyin samun bayanai da kara kyautata tsarin matakan gudanar da aiki.

Gwamna Bala Muhammad ya bayyana cewa bullo da tsarin makarantu mai kunshe da jinsi guda kadai, da daga darajar Cibiyoyin bada ilimin manya mutane don basu dama samun ilimi a karo na biyu, ya tabbatar da bada dama na bai-daya, ya magance takadaranci, ya kyautata kwazon dalibai kuma ya maido da nagartar tsarin ilimin gwamnati a tsakanin iyaye a wannan jiha.

Cikin jawabin Ministan kasa a Ma’aikatar ilimi ta Tarayya Mal. Yusuf Sununu, jinjina wa hangen nesan gwamnatin jiha yayi, bisa bullo da tunanin kiran babban taron kan ilimi, yana mai bada tabbacin goyon bayan gwamnatin tarayya, wajen gani haka ta cimma ruwa.

Ministan yace manufofin ilimi guda takwas da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta kawo, sun hada da kokarin inganta hanyar samar da ilimi mai nagarta, a matsayin wani bangaren kyakykyawar niyyar magance matsalolin da suke ci wa kasar nan tuwo a kwarya.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com