Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labarai

Gwamna Bala Mohammed ya bukaci jama’a su guji rudani da rashin yarda

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na jihar Bauchi ya yi kira ga al’umma da kada su haifar da rudani da rashin yarda a tsakanin ‘yan Najeriya biyo bayan kama wasu da ake zargi da kitsa sace wasu ‘yan asalin jihar su bakwai.

Gwamnan ya yi wannan roko ne a lokacin da ya karbi yaran da aka sace daga rundunar ‘yan sandan jihar a gidan gwamnatin Bauchi bayan an dawo da su gida daga jihar Kano.

Bala Mohammed wanda ya nuna damuwarsa kan abin da ya bayyana a matsayin miyagun sana’o’in da ’yan damfara ke yi ya bayyana cewa ana iya samun irin wannan a kowace kabila a fadin kasar nan.

A yayin da yake nuna rashin jin dadinsa da yadda wasu iyaye ke nuna rashin jin dadinsu na sanya ido kan al’amuran ‘ya’yansu da ke haddasa yawaitar sace-sacen mutane, Gwamnan ya bukaci shugabannin addini da na gargajiya da su wayar da kan su kan hakkin iyaye.

Ya kuma umarci ma’aikatar harkokin mata da ci gaban kananan yara ta jihar da ta gaggauta shigar da yaran makaranta tare da sanar da bayar da gudunmuwar naira miliyan daya ga kowacce daga cikin bakwai da abin ya shafa.

Tun da farko kwamishinan ‘yan sandan jihar Muhammad Auwal wanda ya taimaka wajen dawo da mutanen, ya shaida wa Gwamnan cewa an kama dukkan wadanda ake zargin kuma ana ci gaba da bincike.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com