Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Jiha

Gwaman Jiha Ya Taya Al’ummar Jiha Murnar shiga sabuwar shekara

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya taya al’ummar wannan jiha murnar shiga sabuwar shekarar 2024, yana mai kira a garetaa ta mara baya tare da hadin kai ga gwamnatinsa, don ta samu sukunin kara jan damarar samar da romon demokradiyya.

Cikin sakonsa na sabuwar shekara dauke da sa hanun Mai bashi shawari na musamman kan harkokin yada labarai Comrd Mukhtar Gidado, Gwamnan ya tabbatar da cewa a wa’adinsa na biyu, zaiyi iya bakin kokarinsa wajen ciyar da jiha gaba ta fiskar cigaba da kuma kara inganta yanayin zamantakewa da tattalin arzikin wannan jiha tare da damawa da kowa-da-kowa, a matsayin wata hanyar samar da karin ribar demokradiyya ga jama’a.

Yace gwamnatinsa zata kara zurfafa tuntubar masu ruwa da tsaki da sanya hannayen al’ummu, wadanda su ne madafun gudanar da shugabanci na gari, wanda hakan kuma shi ne manufar kare hakkokin al’umma. Ya kuma taya al’ummar jiha murnar ganin bayan dimbin matsalolin da ta fiskanta a shekarar 2023 da ta gabata, saboda tsayin dakar da tayi wajen fiskantar matsalar tattalin arziki, tabarbarewar muhalli da matsalolin tsaro.

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed, ya kuma bayyana cewa gwamnatin jiha ta yanke shawarin cigaba da wanzar da tsaro, ta hanyar cigaba da sanya ido kan kara-kainan miyagu, yana mai tabbatar da cewa bata-gari da masu mara musu baya ba zasu samu sake ba a Jihar Bauchi, domin gwamnati zata cigaba da baiwa Jami’an tsaro a wannan jiha taimakon da suke bukata yadda ya kamata, don su cigaba da tinkarar matsalolin tsaro a duk lokacin da suka taso.

A cewarsa, gwamnatinsa batayi kasa a gwiwa ba, a kokarinta na samar da gine ginen raya kasa da kyautata rayuwar al’umma, musamman a bangarorin ginin hanyoyi, ginin gidaje, sabunta birane da samar da ilimi mai nagarta, sannan an cimma nasarori masu yawa a bangaren farfado da harkokin noma, tallafin harkokin arziki da kyautata rayuwar matasa.

Don haka yayi kiran cigaba da yin addu’o’i, bada hadin kai da nuna fahimta daga sarakuna, malaman addini, masu ruwa da tsaki da ‘yan siyasa a dukkan bangarori, don dorewar zaman lafiya, kwanciyar hankali da wadata a wannan jiha da kasa baki daya.

 

 

 

Kwamishinan Ma’aikatar yada labarai da sadarwa Comrd Usman Garba Danturaki ya nanata shirin Gwamnatin jiha na cigaba da rike kanbunta na Kwatanniyar yawon shakatawa.

Kwamishinan ya bayyana haka ne yayin biki shiga sabuwar shekara karo na 61, wanda Hukumar kula da Gandun Dajin Yankari ta shirya a masaukin baki na Dajin.

Comrd Danturaki, wanda shi ne Shugaban taron, ya jaddada cewa Gandun Dajin Yankari kafar samun kudin shiga ce abin dogaro ga gwamnatin jiha, don haka akwai bukatar daukan matakan tabbatar da gaskiya da rikon amana a yadda ake gudanar dashi, don cigaban wannan jiha da kasa baki daya.

Kwamishinan ya yaba wa kokarin Gwamna Bala Muhammad, bisa yadda ya samar da yanayi mai kyau wa sashen yawon bude ido da zaman lafiya a wannan jiha, wanda hakan ne yake janyo hankalin masu yawon shakatawa, suke halartar bikin a kowace shekara.

A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar al’adu da yawon bude ido Alh. Abdul Hassan, wanda ya samu wakilcin Babban Sakatare a Ma’aikatar Alh. Sale Mamman, ya baiwa matasa shawarin gudanar da bidirin shiga sabuwar shekara, kamar yadda al’adu da addininsu ya tanada.

A nata bangaren, Kwamishinar Ma’aiakatar Jin kai da magance musibu Hajia Hajara Wanka, ta nanata muhimmancin samar da isassun kudade ne a bangaren yawon bude ido, da nufin samun kudaden shiga, don raya jihar Bauchi.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com