Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Kasa

Gidan Radio Tarayya FRCN zai taimaka wajen karfafa tattakin arzikin kasa.

Ma’aikatar kula da ma’adinan karkashin kasa ta Tarayya da Gidan Rediyon Tarayya – FRCN, suna hada karfi, don tabbatar da ganin Gwamnatin Tarayya ta sake maida hankalinta kan sashen ma’adinai, fadada kafofin tattalin arziki zuwa yankunan karkara.

Minastan inganta ma’adinan Dr. Oladele Alake ne ya sanar da haka, lokacin da yake marabtar Babban Daraktan FRCN Muhammad Bulama a Ofishinsa dake Abuja.

Dr. Alake ya bidi FRCN ta haska sashen ma’adinai sosai a aikinta na yada labarai, yana mai ishara da cewa Ma’aikatar ta samu damar karkatar da hankalin masu zuba jari na gida da waje, zuwa kan albarkatun ma’adinai da Allah Ya huwace wa Nigeria, yana mai tabbatar da cewa, hakan yayi tasiri sosai, kuma ga dukkan alamu, zai haifar da da mai ido. Sannan ya yaba wa Mr. Bulama, bisa kokarinsa na daidaita tsayuwar Gidan rediyon, wanda shi ne sahihin kafar samun labarai da bayanai a kasar nan.

A nasa jawabin, Babban Daraktan FRCN Mr. Muhammad Bulama, ya bayyana Ma’aikatar inganta ma’adinai ta Tarayya, a matsayin wata madogara mai karfi, yana mai yaba wa hobbasa da tayi, wajen kawo sauye sauye, wadanda suka karkato da hankalin duniya, zuwa kan ma’adinan karkashin kasa na Nigeria. Daga nan sai ya tabo wasu daga cikin matsalolin da Gidan Rediyon ke fiskanta, da suka hada da tsoffin kayan aiki, tsarin aikin da aka daina yayinsa, rashin daidaituwar hanyar samun hasken wutar lantarki da ma’aikatan da basu da kuzari a jikinsu.

Don haka ya bidi goyon bayan Ma’aikatar, wajen samun kudade daga Gwamnatin Tarayya, don Gidan Rediyon ya samu damar sauke nauyin da aka dora masa na ilmantarwa da fadakar da ‘yan Nigeria. Sannan yayi alkawarin hada kai da Ma’aikatar inganta ma’adinan, wajen daga darajar kasuwar ma’adinai da wayar da kan al’umma game da sauye sauyen da ake gudanarwa a sashen.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com