Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Duniya

Babban Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya ya gabatarda jawabi mai ratsa jiki

Babban Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mista Matthias Schmale, ya gabatar da jawabi mai ratsa jiki domin bikin ranar Majalisar Dinkin Duniya, wanda ake gudanarwa kowace shekara don tunawa da muhimmiyar ranar da Yarjejeniyar Kafa Majalisar Dinkin Duniya ta fara aiki a ranar 24 ga Oktoba,1945.

A jawabin nasa, babban jami’in ya yi tsokaci a kan ka’idoji da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya da kuma kalubalen da duniya ke fuskanta a yau.

Mr. Schmale ya fara ne da tabo batun yadda aka bude taron Yarjejeniyar Kafa Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya jaddada cewa babban kudirin kafa hukumar shi ne “ceto al’ummar duniya daga bala’in yaki.”

A shekarar 2023, ya bayyana cewa, wannan kudiri na fuskantar kalubalen da ba a taba ganin irinsa ba, inda tashe-tashen hankula suka shafi miliyoyin mutane a wurare kamar Ukraine, Falasdinu, Isra’ila, Sudan da Myanmar, da kuma korar shugaban Nijar da aka yi a kwanan baya.

Babban Jami’in ya bukaci kasashen kungiyar su sake jaddada sadaukarwarsu da girmama Yarjejeniyar ta Majalisar Dinkin Duniya, da kuma sabunta kokarinsu na inganta zaman lafiya, yana mai bayyana cewa, wannan shi ne muhimmin sakon Babban Sakataren MDD Antonio Guterres a bana.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com