Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Addini

ANYI KIRA GA ALKALAN MUSABAKAR AL-QURANI TA KASA DAKE GUDANA A JIHAR YOBE DA SU KASANCE MASU ADALCI WA DALIBAI MASU MUSABAKAR.

Daga Yahuza Yahaya Doka.

An bukaci alkalan Musabakar al-Qurani mai girma ta kasa dake gudana yanzu haka a Damaturu, Fadar jihar Yobe, da su kasance masu kwatanta adalci, wajen baiwa dalibai masu Musabakar maki.

Jami’i Gidauniyar Musabakar karatun al-Qurani ta Nigeria Prof. Mansur Ibrahim Sokoto, wanda yayi kiran yayin fara Musabakar a Damaturu, yace alkalan zasuyi bayanin makin da suka baiwa daliban a gobe kiyama, don haka akwai bukatar su zama masu adalci da gaskiya.

Prof. Mansur Ibrahim Sokoto ya bidi alkalan suyi aiki da abin da al-Qurani mai girma ya kusa, in suna son su kubuta daga korafi, kuma su nemi goyon baya da hadin kan kowa da kowa, don hakarsu ta cimma ruwa. Yana mai kira ga mahalartan su takaitu da ka’idojin Musabakar.

Cikin tsokacin da yayi, Shugaban Kwamitin alkalan Dr Hamisu Kaduna, yayi alkawarin cewa a shirye suke, su baiwa marada kunya. Yana mai karawa da gargadin iyalai da magoya bayan maharta Musabakar, su nisanci aikata duk abin da zai ja hankalin masu musabakar, kuma an haramta wa kowa daukar hoton masu musabakar a lokacin da suke rero ayoyin al-Qurani mai girma.

Dr Hamisu Kaduna ya bukaci mahalartan su siffantu da siffa irin ta musulunci, kuma za’a iya huntasu, in suka aikata wani abin da bai kamata ba a yayin musabakar.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com