Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Jiha

An yi kira ga al’ummar Karamar hukumar Alkaleri da su mara baya ga manufofin Gwamnatin jiha

Abdullahi Mohd Alhaji

Anyi kira ga al’ummar K/hukumar Alkaleri da su cigaba da mara baya wa gwamnatin jiha, don su cigaba da more romon demokradiyya.
Babban Mai baiwa Gwamnan jiha shawari ta fiskar yada labarai Comrade Mukhtari Gidado ne yayi wanna kira, yayin wata Walima da Kungiyar Gangami ta Mukhtari Gidado Door-to-Door ta shirya a Alkaleri, saboda murnar nasarar da Gwamnan ya samu a Kotun koli.
A cewarsa, nasarar ba ta Gwamna Bala Muhammad shi kadai bane, har da al’ummar K/hukumar Alkaleri da Jihar Bauchi baki daya.
Ta bakin Hadiminsa na musamman Mahmmad Nasiru Bappah, Comrade Gidado yayi kira ga mutane kada suyi kasa a gwiwa, wajen yin addu’o’in samun nasara ga Gwamnan, yana mai cewa akwai shirye shiryen aiwatar da karin ayyukan raya kasa a wannan jiha nan ba da jimawa ba, musamman kuma a K/hukumar Alkaleri.
Shi ma cikin jawabinsa Jami’in kare muradun Gwamnan jiha a K/hukumar Alkaleri Bappah Aliyu Alkaleri, ya jinjina wa wadanda suka shirya walimar, kuma ya basu shawarin cigaba da kasancewa masu hadin kai, don cigaban K/hukumar.
A tsokacinsu daban-daban, Babban Limamin Masallacin Kungiayr Izala – JIBWIS na Alkaleri Malam Ahmad Usman da Pastor Bala, sun taya murna wa Gwamnan, game da nasarar da yayi a Kotun koli dake Abuja.
Da suke jinjina wa Gwamnan bisa aiwatar da ayyukan raya kasa masu ma’ana a duk fadin jiha, Shugabannin addinan, sun bayyana gamsuwarsu ga kyakykyawan tunanin wadanda suka shirya walimar.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com