Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
LabaraiLabaran Jiha

AN BUKACI MAMBOBIN MAJALISAR DOKOKI SU SANYA AIKIN CIYAR DA MAZABUN SU GABA

AN BUKACI MAMBOBIN MAJALISAR DOKOKI SU SANYA AIKIN CIYAR DA MAZABUN SU GABA FIYE DA KOMAI NA SON RAAYIN SU.

Mai martaba Sarikin Katagum Dr. Umar Faruq na biyu, yayi kira ga mambobin Majalisar dokokin jiha su jingine batun banbancin siyasa, addinida kabila, a lokacin da suke sauke nauyin mazabunsu daban daban.

Sarkin yayi wannan kira ne lokacin da ya marabci mambobin Kwamitin kula da harkokin K/hukumomi da Masarautu na Majalisar a Fadarsa dake Azare, lokacin da suke cigaba da ziyarar tantance ayyuka a dukkan K/hukumomi 20 na jiha.
Dr. Umar Faruq na biyu, ya tunatar da ‘Yan Majalisar cewa an dora musu alhakin mazabunsu, kuma wajibinsu ne suyi kokarin samar da ayyukan cigaba, don kyautata rayuwar al’ummarsu.

Ya bayyana cewa K/hukuma ita ce tafi kusa, kuma mafi muhimmanci daga cikin matakan gwamnati uku, saboda ita ce mafi kusa da talaka, kuma ya bada tabbacin bada dukkan goyon baya da ya dace da kuma wanzar da bada shawarwari, a duk lokacin da aka bukaci hakan, domin Kwamitin yayi nasarar sauke nauyin da aka dora masa.

A wani labari mai kama da wannan, Kwamitin ya kai kwatankwacin ziyarar a Fadar Mai Martaba Sarkin Jama’are Alh. Nuhu Ahmad Wabi.

Da yake jawabi a yayin marabtar Kwamitin, Sarkin ya bayyana cewa gwamnatin jiha ta amince da bada naira fiye da miliyan 500, don fadadawa da gyaran Fadar Sarkin Jama’are.

Yayi godiya wa ‘Yan Majalisar bisa ziyarar da suka kai masa, kuma ya bukaci su cigaba da mara baya wa manufofi da shirye shiryen Gwamna Bala Muhammad, ba tare da yin la’akari da banbancin Jam’iyyar siyasa ba.

Tun farko, Shugaban Kwamitin Hon. Bala AbdulLahi Dan, yace ziyarar tasu a Fadojin Sarakunan biyu, ta gabatar da kansu ce, a matsayin mambobin Kwamitin na Majalisa ta goma, don kuma bidar tubarraki da shawarwari irin na Uban kasa, don su ji dadin sauke nauyin dake kansu.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com