Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
AddiniLabaran Jiha

An bukaci alkalan gasar karatun kur’ani na jaha da su kasance masu adalci

An bukaci alkalan gasar karatun kur’ani na jaha da ke ci gaba da gudana da su kasance masu adalci wajen bayyana wakilai masu inganci da suka taka rawar gani a lokacin gasar wadanda zasu wakilci jiha a matakin na kasa.

Alarama Abubakar Muhammad Rariya wanda ya yi wannan kiran a wata tattaunawa da gidan Rediyon Bauchi ya ce matukar dai ba a yi zaben ‘yan takara bisa cancantar Jihar Bauchi ba za ta samu wakilci mai kyau a matakin kasa ba.

Wani mai ruwa da tsaki a kwamatin, Alarama Aminu Maisule Zurami ya yi kira ga tawagar da su yi amfani da lokacin wajen yi wa al’umma addu’ar zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki.

Tun da farko shugaban kwamitin gasar karatun kur’ani na jihar Bauchi Imam Hassan Usman Zango ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa yadda aka kammala gasar cikin nasara, ya kuma bukaci ’yan Daliban da su kara kaimi a gasar ta kasa domin jihar ta samu nasara.

A nasa bangaren shugaban kwamitin alkalan gasar Gwani Ashiru Isa Tsoma wanda ya yabawa mahalarta gasar bisa kwazon da suka nuna ya yi alkawarin a shirye su ke su yi hukunci ga mahalarta gasar gwargwadon fahimta.

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com