Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Addini

An bude gasar karatun Alkur’ãni na kasa karo na 38 tare da Yan takara sama da 500

Mahalarta kimanin 500 ne daga jihohi 36 da Babbab Birnin Tarayya Abuja, suka hadu a Damaturu na jihar Yobe, don gudanar da Musabakar al-Qurani mai girma ta kasa karo na 38,tare da yin kira garesu da suyi biyayya ga koyarwar al-Qurani mai girma.

Shugaban Jami’ar Usman Dan Fodio ta Sakwkwato Prof. Lawal Sulaiman Bilbis, wanda yace al-Qurani mai girma na kunshe da dimbin karamomi, yayi kira ga musulmi, musamman matasa, su dabi’antu da al-Qurani, don su samu rayuwa nagartacciya.

Prof. Lawal Bilbis, yace an faro Musabaka ce a shekarar 1983,da nufin jawo hankalin matasa zuwa ga karatu da haddar al-Qurani mai girma yadda ya kamata, da kuma cusa dabi’u da al’adun addinin Musulunci, cikin zukatan matasan.

Yayi amfani da wannan damar, wajen yin kira ga gwamnatin jihar Yobe, ta samar da Cibiyar Musabakar al-Qurani ta kasa tare da abin hawa, yana mai cewa mota guda daya tilo da ake amfani da ita, ita ce wacce tsohon Gwamna Ahmadu Adamu Mu’azu na jihar Bauchi ya bada gudummawarta.
Shi ma Mai alfarma Sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku, wanda ya samu wakilcin Mai Martaba Shehun Barno Alhaji Umar Garbai Elkanemi, kira yayi ga dorewar zaman lafiya da hadin kai tsakanin ‘yan Najeriya.

Cikin tsokacin da bako mai jawabi Professor Abubakar Okene yayi a wajen, yayi kira ga mahaddatan al-Qurani mai girma, su aiwatar da darussan da suka koya.

Da yake bude taron, Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, wanda yayi wa Allah godiya, bisa shaida wannan rana, yace gwamnatinsa a shirye take ta samar da ilimi mai inganci ga matasa

Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana cewar an dauki matakin kafa Hukumar Hisba a jihar, da nufin magance miyagun dabi’u a tsakanin matasa.

Ana sa ran musabakar zata kankama a wannan Asabar 23 ga watan Disamba

DOWNLOAD OUR MOBILE APP Download Our Mobile App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com